Pantami Ya Bayyana Makudan Kudin da Ma'aikatarsa Ta Tattarawa Gwamnatin Tarayya Cikin Shekara 2
- Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, yace ma'aikatarsa na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin kasa
- Pantami yace daga zuwansa ofis shekara biyu da suka gabata ICT ta samar da tiriliyan N1tr
- A cewarsa, a wasu lokutan sai da gudummuwar ICT gwamnatin tarayya take iya biyan ma'aikata albashi
Abuja - Ma'aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani tace ɓangaren fasahar zamani (ICT) zai kara yawan kuɗaɗen shiga da yake samarwa gwamnatin tarayya domin habbaka tattalin arziki, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami, shine ya faɗi haka yayin zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Abuja ranar Lahadi.
Ministan ya jaddada amfani ICT wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya, yace ɓangaren na ICT shine yafi kowane ɓangare cigaba cikin kankanin lokaci.
Premium times ta ruwaito cewa ICT ta samar da kashi 14.7% na kuɗaɗen shiga a Najeriya a shekarar 2020.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane irin cigaba ake samu a bangaren ICT?
Minista Pantami ya kara da cewa Najeriya ta cigaba da tsammanin taka muhimmiyar rawa daga bangaren a nan gaba.
Pantami yace:
"Ku duba kididdigar da hukumar NBC ta fitar a sashen farko na shekatar 2021 (Q1), har yanzun ba'a fitar da na sashi na biyu ba; NBC ta bayyana cewa ɓangaren ICT ya fi kowane ɓangaren cigaba cikin sauri."
"Shugaban ƙasa ya faɗa cewa ICT ta taka muhimmiyar rawa wajen fitar da Najeriya daga karayar tattalin arziki."
"Idan ka duba kuɗaɗen shigar da muka zuba a asusun gwamnatin tarayya zaka tabbatar da haka. Wani lokacin sai da taimakawar ICT ake iya biyan albashi."
Nawa ICT ta tara wa FG a shekara 2?
Dakta Pantami ya kara da cewa daga zuwansa ofis ɗin ministan sadarwa zuwa yanzun bangaren ICT ya samar wa gwamnatin tarayya kudin shiga da suka kai tiriliyan ɗaya.
Ministan yace:
"Zuwa yanzun, bayan na kwashe shekara 2 a ofis, bangaren ICT ya samarwa gwamnati kuɗaɗen shiga da suka kai tiriliyan N1tr."
"Idan kuka duba ƙasafin kuɗin ma'aikatar sadarwa, baya wuce biliyan N5bn. Mu muna samar wa ne mu baiwa wasu ma'aikatu su yi amfani da su."
A wani labarin kuma Sojoji Sun Gargadi Yan Shi'a Mabiya Sheikh Zakzaky Kan Shirin Fitowa Zanga-Zanga
Rundunar sojojin Najeriya ta yi kira ga mabiya akidar shi'a dake shirin zanga-zanga a Jos kada su kuskura su fito.
Sojojin sun ce duba da yanayin da ake ciki a jihar, ba zasu bari a gudanar da irin wannan ayyukan ba.
Asali: Legit.ng