Sojoji Sun Gargadi Yan Shi'a Mabiya Sheikh Zakzaky Kan Shirin Fitowa Zanga-Zanga

Sojoji Sun Gargadi Yan Shi'a Mabiya Sheikh Zakzaky Kan Shirin Fitowa Zanga-Zanga

  • Rundunar sojojin Najeriya ta yi kira ga mabiya akidar shi'a dake shirin zanga-zanga a Jos kada su kuskura su fito
  • Sojojin sun ce duba da yanayin da ake ciki a jihar, ba zasu bari a gudanar da irin wannan ayyukan ba
  • Kwamandan Operation Safe Haven ya umarci jami'an soji da su hana yin zanga-zangar a Filato

Jos, Plateau - Rundunar sojojin Najeriya ta gargaɗi mabiya aƙidar shi'a kan fitowa zanga-zanga a dukkan sassan jihar Filato, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Rundunar ta yi gargaɗin ne a wata sanarwa da kakakin sojojin Operation Safe Haven, Ishaku Takwa, ya fitar.

Kungiyar mabiya akidar shi'a (IMN), wadda Sheikh Ibrahim El-Zakzaky yake jagoranta, suna shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin kasa.

Sojoji sun gargadi yan shia
Sojoji Sun Gargadi Yan Shi'a Mabiya Sheikh Zakzaky Kan Shirin Fitowa Zanga-Zanga Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Meyasa yan shi'a zasu fito zanga-zanga?

Sanarwar sojojin tace:

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

"Mun samu rahoton cewa yan kungiyar IMN da aka fi sani da yan shi'a suna shirin fita kan tituna yin zanga-zanga, kuma an shirya ta ne a faɗin kasar nan baki ɗaya."
"Sun shirya gudanar da zanga-zangar a Filato ranar Jumu'a saboda rashin lafiyar jagoransu Al-Zakzaky. Kowane ɗan kasa ya na da damar yin zanga-zanga ta lumana."
"Amma bisa dalilin yanayin da ake cikin a jihar Filato, ba zai yuwu a yi irin waɗannan abubuwan ba."

Meyasa sojoji suka hana yan shi'a?

Takwa ya kara da cewa kwamandan rundunar Operation Safe Haven, Ibrahim Ali, ya umarci sojoji da su dakatar da yan shi'an har sai an tabbatar da komai ya koma dai-dai.

Punch ta ruwaito Takwa yace:

"Mun samu rahoto cewa akwai wasu bara gurbi dake shirin amfani da wannan zanga-zangar su tada hargitsi a cikin garin Jos da kuma wasu yankuna."

Kara karanta wannan

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona

"Saboda haka muna kira ga mambobin kungiyar IMN da su dakatar da shirin su na yin zanga-zanga a faɗin jihar Filato."

A wani labarin kuma Duk Mai Son Gani Bayan IMN Zai Sha Kunya, Sheikh Zakzaky Ya Yi Jawabi Na Farko Bayan Shakar Iskar Yanci

Shugaban kungiyar mabiya akidar shi'a (IMN), Sheikh IbrahIm El-Zakzaky, ranar Talata yace duk mai son wargaza tafiyarsa ba zai ci nasara ba.

Zakzaky yayi wannan maganar ne a taronsa na farko da wakilan kungiyarsa na jihohi da wasu kungiyoyi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel