Daurin auren Yusuf Buhari: Jiragen Alfarma fiye 25 ne suka dira a Kano, Ƴan Nigeria sunyi martani

Daurin auren Yusuf Buhari: Jiragen Alfarma fiye 25 ne suka dira a Kano, Ƴan Nigeria sunyi martani

  • Biki ya yi biki don akalla jiragen sama na alfarma guda 20 cike da manyan mutane suka isa Kano daurin auren dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf
  • Rahotanni sun tabbatar da yadda kushoshin da ake ji dasu a fadin Najeriya har da ketare suka cika filin jirgin Malam Aminu Kano da jirage na alfarma alfarma
  • Cikin manyan masu ji da isa akwai Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya, mataimakon shugaban kasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon shugaban kasar Nijar Muhammadu Isoufu da sauransu

Jihar Kano - Akalla jiragen sama na alfarma guda 25 cike da kasaitattun mutane masu fadi aji a fadin Najeriya har da ketare suka dira jihar Kano don shaida daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko

Yusuf, da daya tilo na Buhari ya auri Zahra ne, diyar sarkin Bichi, Mai martaba Nasir Ado Bayero.

Daurin auren Yusuf Buhari: Jiragen Alfarma fiye 25 ne suka dira a Kano, Ƴan Nigeria sunyi martani
Jiragen Sama na alfarma da suka dira a Kano don daurin auren Yusuf Buhari. Hoto: @arewafamilyweddings
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wakilin Daily Trust ya kirga akalla jiragen sama na alfarma guda 20 da ya gani a filin jirgin Malam Aminu Kano a ranar Juma'a 20 ga watan Agusta da aka daura auren.

Daurin auren Yusuf Buhari: Jiragen Alfarma fiye 25 ne suka dira a Kano, Ƴan Nigeria sunyi martani
Jiragen Sama na alfarma da suka dira a Kano don daurin auren Yusuf Buhari. Hoto: @arewafamilyweddings
Asali: Instagram

Wasu daga cikin manyan bakin da suka hallarci daurin auren

Manyan mutane masu ji da kansu sun halarci gagarumin daurin auren.

Cikinsu akwai tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan da tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadu Isuofu.

Saura sun hada da mataimakin shugaban kasan Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Aminu Tambuwal daga Sokoto, Abdullahi Ganduje na Kano, Babagana Umara Zulum na jihar Borno da sauransu.

Abin da wasu yan Nigeria suka ce game da bidiyon jiragen saman na alfarma

Kara karanta wannan

Hotunan shagalin 'Luncheon' na auren Yusuf Buhari da amaryarsa Zahra Bayero

Ga wasu abubuwan da masu amfani da shafin instagram suka ce game da bidiyon jiragen.

Bxbbayy ya ce:

"Da hakan kuma wasu ke da karfin zuciyar fada mana babu kudi a Nigeria"

prince_khalid_usman ya ce:

"Kuma suna fada mana babu kudi a Nigeria."

Zainabgilima ta ce:

"Ban taba ganin filin tashi da saukan jirage na Kano ya cika makil haka ba, musamman bangaren jiragen yawo. MashaAllah."

Tsabar Cin Bashi: Majalisar Wakilai ta yi wa Buhari Wankin Babban Bargo

A wani labarin daban, majalisar wakilai ta nuna alhininta a kan yadda wasu bangarorin gwamnati suke adana kudin shigarsu da suke tarawa suna barin gwamnatin tarayya da nemo kudin kasafi.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda majalisar ta soki yadda gwamnati ta ketara kasar waje don cin bashin naira tiriliyan 5.62 don cikasa kasafin shekarar 2022, yayin da wadannan bangarorin gwamnatin suke killace kudaden a asusansu.

James Faleke, shugaban kwamitin majalisar a fannin kudade ya bayyana hakan ne a wani taro na sauraron MTEF da FSP na shekarar 2022 zuwa 2024 a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

Hotunan Aisha Buhari lokacin da take jiran isowar amaryar dan ta Yusuf Buhari

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel