A karshe ‘yan sanda sun cafke shahararrun masu garkuwa da mutane da ke addabar jihar Adamawa

A karshe ‘yan sanda sun cafke shahararrun masu garkuwa da mutane da ke addabar jihar Adamawa

  • Jami'an 'yan sanda a Adamawa sun fasa mabuyar shahararrun masu garkuwa da mutane da ke addabar jihar
  • DSP Sulaiman Nguroje, mai magana da kakakin ‘yan sandan jihar, wanda ya bayyana haka a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, ya bayyana cewa an kama akalla masu garkuwa da mutane 14
  • Nguroje ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun yarda cewa sun amshi makudan kudade a matsayin kudin fansa daga wadanda suka sace

Adamawa, Yola - 'Yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da cafke wasu mutane 14 da ake zargin shahararrun masu garkuwa da mutane ne da ke addabar mutanen jihar.

Vanguard ta rahoto cewa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 17 ga watan Agusta a Yola, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

A karshe ‘yan sanda sun cafke shahararrun masu garkuwa da mutane da ke addabar jihar Adamawa
Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba Hoto: Nigeria Police.
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Nguroje ya ce nasarar ta biyo bayan sahihan bayanai daga majiyoyi masu tushe.

An damke wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kananan hukumomi uku

Nguroje ya ce an kama wadanda ake zargin a kananan hukumomin Fufore, Yola ta Kudu da kuma Jada na jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce a yayin da ake gudanar da tambayoyi duk wadanda ake zargin sun amsa laifin sace wani Alhaji Sale Idi na Farang a karamar hukumar Fufore da Ya’u Adamu na garin Ganye a karamar hukumar Ganye.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya lura cewa wani wanda abin ya rutsa da shi shine Jones Hayatu na kauyen Kojoli a karamar hukumar Jada, ya kara da cewa masu garkuwar sun kuma amince da karbar makudan kudade a matsayin kudin fansa daga wadanda abun ya cika da su.

Kara karanta wannan

Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

The News ya kuma ba da rahoton cewa Nguroje ya ce kwamishinan ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai dangane da duk wani mutum da ake zargi a unguwarsu ga 'yan sanda.

Ya ci gaba da ba da umarnin a gudanar da bincike cikin hankali tare da ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda ake zargi da laifi.

Barayin da Suka Sace Malamai, Dalibai a Kwalejin Zamfara Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N350m

A wani labarin, yan bindigan da suka sace malamai da ɗalibai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura, jihar Zamfara, sun nemi a basu miliyan N350m kuɗin fansa.

Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntuɓe shi ta wayar salula.

Yace yan bindiga sun nemi a ba su miliyan N350m kuɗin fansar mutum 20 dake hannun su a yanzun sannan su sako su.

Kara karanta wannan

Gada ta ruguje a Jigawa, ta hallaka matafiya ciki har da masu neman aikin soja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng