Bata-gari sun sheke mai POS bayan yi mishi fashin N4m a Ogun

Bata-gari sun sheke mai POS bayan yi mishi fashin N4m a Ogun

  • Hukumar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wasu mutane 4 wadanda suka yi wa wani mai POS fashin naira miliyan 4
  • Ba a nan suka tsaya ba, daga baya suka lallaba suka bi shi suka hallaka shi daga nan suka babbaka gawarsa
  • Wani Aanu Salaudeen ne ya kai korafi ofishin ‘yan sanda dake Onipanu a ranar 18 ga watan Augustan 2021

Ogun - Jami’an hukumar ‘yan sanda sun kama mutane 4 da ake zargin suna da hannu da yi wa wani mai POS, Abiodun Odebunmi, fashin naira miliyan 4 kuma daga baya suka hallaka shi kuma suka babbaka gawarsa.

Wadanda ake zargin sune wani Kehinde Saliu Jelili (wanda akafi sani da Oluomo), Abiodun Akinola, Johnson Fakeye da Jamiu Akinola, wadanda aka ce sun yi fice a wurin fashi da hallaka masu POS da UBER.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyon mutumin da ya auri mata biyu a rana daya, an yi masu ruwan N20

Bata-gari sun sheke mai POS bayan yi mishi fashin N4m a Ogun
Bata-gari sun sheke mai POS bayan yi mishi fashin N4m a Ogun. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya aka yi miyagun suka shiga hannu?

An kama dukansu bayan wata Aanu Salaudeen ta mika korafinta ga ofishin ‘yan sandan dake Onipanu a ranar 18 ga watan Afirilun 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wacce ta kai korafin ta sanar da ‘yan sanda cewa taje shagon POS din wani Abiodun Adebunmi bayan ta bar oganta na wurin aiki a ofishinsu dake Aparadina ana gobe hakan za ta faru don ta ciri naira miliyan 4 don a yi amfani dasu wurin harkar POS.

A cewarta bata ga Abiodun Adebunmi ya koma gida ba kuma ta kira wayarsa amma bata shiga.

A cewara, dama sun taba yin cinikin naira miliyan 1.5 da wani mutum wanda ya gayyaci shugabansa washegari, bayan nan ne shugaban nasa yace su hadu a Ojuore don su yi wata harkar POS din ta naira miliyan 4.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

Oyeyemi ta sanar da manema labarai a ranar Alhamis cewa bayan ta bayar da rahoton ne ‘yan sandan Onipanu suka fara bincike a kan yadda aka nemi mutumin aka rasa.

A cewarta duk wasu kokarin da za su yi sun yi amma ya tashi a tutar babu bayan sun tsinci babbakakkar gawar mutumin a wani kangon gini a wuraren Arobieye dake Ota ba tare da ganin sawun wadanda suka hallaka shi ba.

Oyeyemi ya ce an dauke korafin an mayar bangaren bincike na musamman bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda, Edward Awolowo Ajogun.

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

Prince Samuel Adedoyin, wani hamshakin biloniya dan asalin jihar Kwara ya rasa diyarsa, Princess Lola Olabayo.

Mummunan lamarin ya faru ne yana tsaka da jimamin mutuwar dansa Subomi da watanni biyu bayan ya yi ajalin kansa, duk da dai ba asan dalilinsa nayin hakan ba.

Kara karanta wannan

Sunayen Matafiya fiye da 20 da aka yi wa kisan gilla a Jos, wani ya rasa 'yanuwansa 7

An samu labarin yadda ta rasu a asibitin jihar Legas bayan kwashe kwana 7 kwance sakamakon fama da cutar COVID-19.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel