Hotunan shagalin 'Luncheon' na auren Yusuf Buhari da amaryarsa Zahra Bayero
- Shugaba Buhari ya halarci shagalin Luncheon da aka shirya a bikin dansa Yusuf da Zahra Bayero
- A jiya ne aka kai amarya Abuja, wanda a yau kuma aka shirya kasaitaccen bikin na Luncheon
- Legit Hausa ta tattaro muku hotunan wannan shagali domin kada ayi biki babu mabiyanmu
Abuja - A ci gaba da shagalin bikin dan shugaba Buhari Muhammadu na Najeriya; Yusuf da kuma 'yar sarkin Bichi Alhaji Nasiru Bayero; Zahra, an yi kasaitacciyar liyafar Luncheon a babban birnin tarayya Abuja.
A ranar juma'ar da ta gabata ne aka daura dauren masoyan biyu, inda aka samu haartar masoya daga sassa daban-daban na Najeriya da ma duniya baki daya.
An gudanar bikin Luncheon da ya samu halartar shugaban kasa da sauran manyan Najeriya, ciki har da jiga-jigan siyasa da ake damawa da su a kasar.
Jerin wasu daga cikin wadanda suka halarci shagalin
Buhari Sallau, wani mai taimakawa shugaban kasa a fannin yada labarai, ya bayyana wasu daga cikin wadanda suka halarci shagalin a shafinsa na Facebook.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo
- Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan
- Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Bayero
- Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha
- Uwar gidan shugaban kasa, uwar ango; Aisha Buhari
- Uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Ladipo Osinbajo
- Uwar gidan shugaban kasar Nijar
- Uwar gidan shugaban kasar G/Bissau
- Matan gwamnoni da sauran manyan baki
Legit Hausa ta tattaro hotunan bikin Luncheon din da ya gudana.
Kalli hotunan:
Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' na Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari
A wani labarin, A rana ta hudu a farin cikin bikin dan shugaban kasa, Yusuf Buhari da 'yar sarkin Bichi, Zahra Nasir Bayero, an yi shagalin budan kai jiya Asabar 21 ga watan Agusta.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka daura auren Yusuf Muhammadu Buhari da ga shugaban kasar da Najeriya da kuma Zahra Nasir Bayero 'yar sarkin Bichi.
Ana ci gaba da shagalin biki, yayin da jiya Asabar ta kasance rana ta hudu a jerin jadawalin shagulgulan da ake gwangwajewa na bikin.
Asali: Legit.ng