Da duminsa: Buhari ya dira Kano don halartan daurin auren 'dansa Yusuf

Da duminsa: Buhari ya dira Kano don halartan daurin auren 'dansa Yusuf

  • Daga Adamawa, shugaba kasa ya garzaya jihar Kano kai tsaye
  • Buhari ya tafi Adamawa ne don ta'aziyyar Alhaji Ahmad Joda
  • Za'ayi daurin auren 'dan gidan Buhari a Bichi

Kano - Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Kano daga Adamawa domin halartan daurin auren dansa daya tilo, Yusuf Buhari, da za'a yi a kasar Bichi.

Hadimin Buhari kan gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya sanar da hakan ranar Juma'a.

A yau aka shirye daura auren Yusuf Buhari da diyar Sarkin Bichi, Zahra Bayero, a yau Juma'a a kasar Bichi.

Shugaba Buhari Ya Tura Wakilai Na Musamman Zuwa Kano

Tuni dai Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tura tawagar wakilai na musamman domin ɗaura auren ɗansa, Yusuf da Zahra, ɗiyar sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daurin auren Yusuf Buhari: Jiragen Alfarma fiye 25 ne suka dira a Kano, Ƴan Nigeria sunyi martani

Tawagar wakilan, bisa jagorancin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, zata je Kano ne domin halartar ɗaura auren.

Su waye wakilan da Buhari ya tura?

Tawagar fadar shugaban ƙasan sun haɗa da ministoci kamar ministan tsaro, Bashir Salihu Magashi.

Sannan akwai ministan noma, Alhaji Sabo Nanono, Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, da kuma ministan albarkatun ruwa, Hussein Adamu.

Sai dai bayan kammala ɗaura auren, Mallam Garba Shehu zai tsaya ya wakilci shugaba Buhari a wurin taron mika sandar mulki ga sarkin Bichi.

Fani-Kayode yayin da ya shiga sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Buhari

Duk da adawarsa da Buhari, Femi Fani-Kayode, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, ya shiga cikin wasu manyan jiga-jigan ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin daurin auren Yusuf.

Kara karanta wannan

Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa dan Shugaba Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu, an yi cece-kuce

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel