Maƙwabciya na ta sharara min mari domin ta ga abin da matata za ta yi, Magidanci ya faɗa wa kotu

Maƙwabciya na ta sharara min mari domin ta ga abin da matata za ta yi, Magidanci ya faɗa wa kotu

  • Wani Akor Kenneth ya bayyana wa wata kotu dake Abuja cewa makwabciyarsa, Juliana Umana ta sharara masa mari don ta ga abinda matarsa zata iya
  • Ya bayyana yadda lamarin ya kasance inda yace suna tsaka da tattaunawa da makwabtansa don ganin yadda za su gyara kwatar dake unguwarsu ta sharara masa marin
  • Bayan aukuwar hakan ne ta bayyana masa cewa ta zabga masa marin ne musamman don ta janyo matarsa su gwabza dambe kuma ta ki bashi hakuri

Kubwa, Abuja - Wani likitan dabbobi mai shekaru 37, Akor Kenneth, ya sanar da kotu mai daraja ta daya dake Kubwa a Abuja cewa wata makwabciyarsa, Juliana Umana ta sharara masa mari don ta ga yadda matarsa za ta yi.

Vanguard ta ruwaito cewa, ‘yan sanda sun damki Umana da laifin cin zarafi da wulakanci.

Kara karanta wannan

Matata ta yi barazanar sheƙe ni har lahira da adda, Magidanci ya sanar da kotu

Lauyan mai kara, Babajide Olanipekun, ya ce Kenneth yana zaune ne a Arab Road extension dake Kubwa a Abuja.

Maƙwabciya na ta sharara min mari domin ta ga abin da matata za ta yi, Magidanci ya faɗa wa kotu
Maƙwabciya na ta sharara min mari domin ta ga abin da matata za ta yi, Magidanci ya faɗa wa kotu. Hoto daga Vanguard News
Asali: Facebook

Yadda al'amarin ya kasance

Mun fuskanci matsala a magudanun ruwa a anguwarmu, hakan yasa na nemi mijinta don mu tattauna a kan matsalar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar 10 ga watan Nuwamban 2020 muna tsaka da tattaunawa da sauran makwabta a kan matsalar, Juliana ta lallabo ta sharara min mari a gaban mijinta da sauran makwabtanmu guda biyu.
Ta bayyana min cewa ta mare ni ne musamman don ta nemi matata da fada, a cewarsa.

Kenneth ya bayyana yadda ya bar wurin bayan ya tsaya yana jiran ta bashi hakuri amma ta murje idanunta taki.

Bayan naga bata bani hakuri bane yasa na kawo kararta ofishin ‘yan sanda dake Byazhin, a cewarsa.

Alkalin ya amshi shaidar da mai kara ya bayyana.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Alkalin, Muhammad Adamu ya daga sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Satumba.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

A wani labari na daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: