Matata ta yi barazanar sheƙe ni har lahira da adda, Magidanci ya sanar da kotu

Matata ta yi barazanar sheƙe ni har lahira da adda, Magidanci ya sanar da kotu

  • Wani John Ifedinkor ya sanar da wata kotu dake Abuja cewa matarsa Ngozi ta yi yunkurin ganin bayansa
  • Kamar yadda ya tabbatar wa da alkali, ta yi amfani da adda ne wurin hallaka shi bayan wata hayaniya da suka yi
  • Bayan ganin ta zaro dalleliyar addar ne yasa yayi gaggawar garzayawa ofishin ‘yan sanda ya kai korafi

Abuja - Wani magidanci John Ifedinkor mai shekaru 59 ya sanar da wata kotu dake Kubwa dake Abuja cewa matarsa Ngozi ta yi kokarin kassarasa da adda, Daily Nigerian ta ruwaito.

Tuni ‘yan sanda suka kama Ngozi bisa zargin ta da yunkurin aikata mugun aiki.

Ya bayyana wa kotun hakan ne ta bakin lauyansa, Babajide Olanipekun, inda Ifedinkor ya sanar da yadda Ngozi ta zaro dalleliyar adda bayan sun gama wani sa-in-sa a ranar 13 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Matata ta yi barazanar sheƙe ni har lahira da adda, Magidanci ya sanar da kotu
Matata ta yi barazanar sheƙe ni har lahira da adda, Magidanci ya sanar da kotu. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC
Lokacin da na tambaye ta dalilin da yasa take kunna murhun mu da daddare sai ta dauko turmi da tabarya ba tare da ta sanya wani abu ciki ba ta hau daka. Sai na hassala na umarce ta da ta daina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Take a nan ta shige daki ta dauko adda ta samu waka tana wasa ta da ita. Take a nan matata ta yi yunkurin hallaka ni da addar,” a cewar Ifedinkor.
Bayan nan ne nayi gaggawar sanar da hukumar ‘yan sanda a ofishinsu dake Kubwa.

Ta dade tana yunkurin halaka ni, Magidanci

Ifendikor ya kara da bayyana yadda ta dade tana yunkurin ganin bayansa da yaransu ta hanyar amfani da guba.

Masu karbar kara sun mika bayanin da Ifedinkor yayi musu a gaban kotu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Alkalin kotun, Muhammad Adamu ya dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Oktoba don a kara dubar lamarin.

Kara karanta wannan

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

Kaman Dirama: Yadda Ƴan Sanda Suka Sha Mugun Duka a Hannun Ƴan Banga Saboda Ganyen Wiwi

A wani labari na daban, kungiyar Edo Security Network ta yan banga a jihar, ta kama yan sanda biyu kan zargin samunsu da wani ganye da ake zargin wiwi ne a jihar ta Edo, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan banga sun kama yan sandan ne a Oko-Ogba a hanyar zuwa filin tashin jiragen sama da ke Benin, babban birnin jihar yayin wani bincike da suke yi a hanyar.

Yan bangan sun bincika mota kirar Lexus mai rajista RX330 ne da daya daga cikin yan sandan ke tukawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel