'Yan bindiga sun sace malaman jami'ar ABSU ciki har da Farfesa

'Yan bindiga sun sace malaman jami'ar ABSU ciki har da Farfesa

  • 'Yan bindiga sun sace wasu mutane ciki har da malaman jami'ar ABSU ta jihar Abia
  • 'Yan bindigan sun sace su ne yayin da suka tare hanya suna yi wa mutane fashi da makami
  • Shugaban kungiyar ASUU, reshen ABSU, V.U. Nkemdirim ya tabbatar da lamarin ya kuma ce an sanar da hukumomin tsaro

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace malamai biyu na Jami'ar Jihar Abia, ABSU, da ke Uturu da wasu mutanen a kan hanyar ABSU-Isuikwuato, News Wire NGR ta ruwaito.

Shugaban kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, reshen jami'ar ABSU, V.U. Nkemdirim ne ya sanar da sace su a ranar Juma'a.

'Yan bindiga sun sace malaman jami'ar ABSU ciki har da Farfesa
'Yan bindiga sun sace malaman jami'ar ABSU ciki har da Farfesa. Hoto: The Punch
Asali: Depositphotos

A cewar Nkemdirim, lamarin ya faru ne misalin karfe 6 na yamma a ranar Alhamis kamar yadda News Wire NGR ta ruwaito.

Ya ce wadanda aka sace din sune Rebaran Farfesa S.O. Eze na tsangayar Industrial Chemistry da kuma wani malamin coci, kuma malami a tsangayar koyar da fasahar sadarwa, Chris Afulike.

Ta yaya aka sace malaman?

An ce kowannensu na tafiya a motarsa daban ne yayin da suka fada hannun yan bindigan da suke tare hanya suna yi wa matafiya fashi.

Malamin jami'ar ya ce:

"Bayan fashin, yan bindigan sun yi awon gaba da malaman jami'an biyu da wasu mutane.
"Kawo yanzu ba a san inda suke ba. Amma, an gano motar Dr Chris Afulike kirar Toyota Camry da wayarsa ta salula a cikin motar."

Nkemdirim ya kara da cewa iyalan malaman jami'an sun tabbatar da afkuwar lamarin, kuma mahukunta a jami'ar suma suna bada gudunmawa domin ganin yadda za a ceto su.

Ya kara da cewa an sanar da mahukunta ASUU na kasa da kuma sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa.

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel