Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4

Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4

An taba ware wata rana guda a shekarar 1962 da aka gudanar da babban taron matan nahiyar Afirka a birnin Dar-es-Salam dake kasar Tanzania.

Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4
Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4

Tun bayan dakatar da tsarin cinikin bayi da cin zarafin matan yankin Afirka, mata sun samu daman damawa a duk lamurran da suka shafi mutane, walau na siyasa ko na shugabanci ko na kasuwanci. Don haka ne a yau muka kawo muku takaitattun tarihin hamshakan sarakuna mata da aka taba yi a nahiyar Afirka.

1.Sarauniya NERFETITI

Nerfetiti itace sarauniya da tafi shahara a nahiyar Afirka, kamar yadda tarihi ya nuna sakamakon tsananin kyawunta daya sanya ta shahara, Nerfetiti itace uwargidar Sarkin Fir’auna Akhenaten na 18, hakan ya sanya ta kasancewa uwar dakin Fir’auna Tatankhamun.

Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4
Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4

Nerfetiti tayi suna ne saboda zanen gunkin ta wanda a yanzu haka ke ajiye a dakin adana kayan tarihin na birnin Berlin a kasar Jamus wanda fasihin mai zane Thutmose ya kera. Duk wanda ya ga wannan gunkin na Nerfetiti zai shaida kwarewar masu zanen kasar masar tun a zamanin baya.

Sakamakon suna da shahara da sarauniya Nerfetiti tayi a Duniya, hakan ya sanya ta samun sunaye daban daban a kasashe daban daban, misali a kasar Italiya ana kiranta ‘magajiya’, wasu kuma na yi mata kirari da ‘mai samar da kwanciyar hankali’, ko ‘uwar dakin kafatanin masarautar Masar’, wasu suce mata ‘mai babban dakin masarautar Masar’, ana ce mata ‘uwar garuruwa biyu’ sa’annan ana kiran ta da ‘Nerfetiti’.

Wani muhimmin aikin da Nerfetiti tare da mijinta suka gudanar a zamaninsu shine tabbatar da bautan Allah shi kadai a kasar Masar.

KU KARANTA:Wata mata ta haifi yan Uku a sansanin ýan gudun hijira

2.Sarauniya Amina, ta Zaria

Sarauniya Amina wanda ta rayu a tsakanin shekarun alif dari shidda zuwa alif dari bakwai jaruma ce matuka yarinyar sarkin Zazzau Turunku.

Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4

Amina ta fafata a yakoki da dama wajen mamayewa tare da cin garuruwa da dama yakuna don samun daman kara baza mulkin tad a kara ma harkokin kasuwancin ta karfi.

Sai dai Amina bata taba yin aure ba, inda tace muddin tayi aure, ta san zata rasa karfin iko irin na mulki, hakan ya sanya Amina a koda yaushe idan ta ci gari da yaki, sai ta zabo namiji karfaffa ta kwanta da shi, gari na wayewa sai ta kashe shi, saboda kada ya ba kowa labarin ta.

3.Sarauniya Peggielene Bartels, ta Ghana

Sarauniya Peggeielene na daya daga cikin sarakunan zamanin nan a kasar Ghana, wanda nan ba da dadewa ba ta taba yin aikin a matsayin sakatariya a kasar Amurka.

Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4

Amma cikin ikon Allah farar daya wata rana a shekarar 2008 aka kira ta a waya inda aka shaida mata cewar kawunta Sarki ya rasu, don haka gidan Sarauta na Bartel ne zasu hau karagar mulki, da wannan ne ta zama Sarauniya ta farko a kasar Ghana.

Sarauniya Bertel tayi karatun digiri a jami’ar Ingila, daga nan ta koma kasar Amurka inda ta samu shaidar zama dan kasa a shekarar 1997, bayan ta zama Sarauniya ne aka nada ta mukamin sakatariya ta biyu a ofishin jakadancin kasar Ghana a Amurka.

A duk shekara tana gudanar da zaman fada sau daya, inda a wannan lokaci ne take warware matsalolin da suka gagari hakimanta, ta kan yi shiga irin na saraki a wannan lokaci, kuma tana taimaka ma makarantu da asibitoci da kayayyakin aiki wadanda take samowa daga kasar Amurka.

4.Sarauniya Dihya

An dan samu cece kuce tsakanin masana da dama dangane da asalin ma’anar sunan sarauniya Dihya, inda wasu suka ce ai suna ne irin na yahudu, amma mabiyanta sun bayyana ma’anarsa a matsayin kyakkyawa.

Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4

Yayin da wasu ke ikirarin cewar Dihya yar kabilar Bereber ce da suka rikida suka canza addini zuwa addinin yahudu, wato Judaism, wasu kuma suka ce a’a, ai Dihya yar kabilar Berber ce masu addinin kirista, har ilau wasu sun ce Dihya yar talakawar kabilar yahudawa ce mazauna koguna, kuma ma sunan ubanta Tobit ko a ce Tuvia.

Masana tarihi sun bayyana sarauniya Dihya a matsayin cikakkiyar mace, mai tsawo, baka, dara dara idanu da dogo kuma bakin gashi.

Tarihi ya bayyana cewar wata rana Dihya ta nufi shuwagabannin kabilar Berber dake rike dasu a matsayin bayi, sai shugaban kabilar ya ganta yace zai aure ta, ita kuwa Dihya ta yarda ta aure shi, amma a daren aurensu Dihya ta kashe shi, kuam tayi juyin mulki.

Shahararren Masanin tarihin nan Ibn Khaldun ya bayyana cewar Sarauniya Dihya ta kwashe shekaru 127 a rayuwa, inda tayi mulki na tsawon shekaru 60.

5.Sarauniya Sakhmakh, ta masarautar Nubia

Sarauniya Sakhmakh ta kasance uwargidar Sarkin Kushite, Fir’auna Nastasen wanda yayi zamani tun kafin zuwan Annabi Isah.

Tarihin Sarauniya Amina ta Zaria da makamantan ta guda 4

Masana sunce Sakhmakh na nufin ‘yarinyar Sarki, matar Sarki ko budurwar Sarkin Masar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng