Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Yola don gaisuwar ta'aziyyar Ahmad Joda
- Shugaba kasa ya tafi jihar Adamawa yau Juma'a
- Jihar Adamawa ta yi rashin manyan 'yayanta uku a kwanakin nan
Yola - Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Yola, jihar Adamawa a ranar Juma'a, 20 ga Agusta, domin gaisuwar ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Ahmed Joda.
Buhari ya dira ne misalin karfe 10 na safe tare da tawagarsa.
Hadimin Buhari na gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya bayyana haka.
Dirarsa ke da wuya, Buhari ya garzaya fadar Lamidon Adamawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rasuwar Alhaji Ahmad Joda
Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Najeriya lokacin mulkin Soja kuma mutum na farko da Buhari ya ba mukami bayan nasara a 2015 , Alhaji Ahmed Joda, ya mutu.
Ya rasu ne ranar Juma'a, 13 ga Agusta a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.
Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.
Alhaji Ahmed Joda ya cika ne yana mai shekaru 91 a duniya.
Joda ya yi karatunsa a Najeriya da kuma Birtaniya inda ya halarci Kwalejin Pitmans da ke birnin London daga 1954 zuwa 1956.
Ya rike kujeran sakataren din-din-din lokacin gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon (Mai murabus).
Asali: Legit.ng