Kayatattun Hotuna da Bidiyoyin Shagalin Kamun Gimbiya Zahra Bayero da Yusuf Buhari
- Auren gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari da za a kulla da na masarautar Bichi ya dauka kala
- A ranar Laraba da ta gabata ne masarautar Bichi ta shirya gawurtaccen bikin kamu domin amarya Zahra da angonta Yusuf
- Amarya Zahra Bayero ta sha kyau inda aka ganta tare da angonta, zagaye da 'yan uwanta da kuma dangin ango
Bichi, Kano - Biki tare da shagali ya kankama a masarautar Bichi ta jihar Kano. Tuni manyan mutane masu alfarma suka fara hallara gawurtaccen bikin da za a yi tsakanin da namiji daya tilo na gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Bayero, jikar basarake da yayi zamani mai birgewa, Alhaji Ado Bayero.
A jiya ranar Laraba ne masarautar Bichi ta shiryawa Gimbiya Zahra Nasir Bayero kasaitaccen bikin kamun bikinta da za a yi a ranar Juma'a mai zuwa.
Ba 'ya'yan sarakuna kadai suka samu damar halarta ba, an ga hotunan 'ya'yan shugaban kasa Muhammadu Buhari da suka hada da Halima, Zahra Indimi tare da auta Noor Muhammadu Buhari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babu shakka amarya Zahra Bayero ta sha matukar kyau inda tayi shiga cikin wasu kaya masu nau'in shudaye tare da alkyabba mai launin shudin wacce ta ji adon zare launin zinari.
Daga cikin hotuna da bidiyon da shafin da aka bude domin kawo labaran bikin kai tsaye mai suna @thebeginningofyz suka wallafa a Instagram, an ga mahaifin amarya, Mai Martaba Alhaji Nasir Ado Bayero a cikin shigarsa ta alfarma tare da 'ya'yansa.
A daya daga cikin bidiyoyin kuwa, an ga mai martaban tare da amarya da ango inda suke shirin daukar hoto sannan yana gyarawa diyarsa alkayabba, lamarin da ya matukar birge masu kallo.
Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong
Simon Lalong, gwamnan jihar Filato ya bayar da umarnin damke duk wanda yayi gaggawar zuwa belin wandanda aka kama ana zargin suna da hannu a kan farmakin jiharsa.
Gwamnan jihar ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron gaggawa da yayi da manyan jami’an tsaro a Jos, Thecable.ng ta ruwaito.
Kamar yadda NAN ta ruwaito, an yi taron na musamman ne a ranar 14 ga watan Augusta akan harin da aka kai karamar hukumar Bassa, Jos ta kudu, Barikin Ladi da Riyom.
Asali: Legit.ng