Jam'iyyar APC Ce Zata Lashe Zaben Gwamnan Anambra Dake Tafe, Uzodinma

Jam'iyyar APC Ce Zata Lashe Zaben Gwamnan Anambra Dake Tafe, Uzodinma

  • Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana cewa yana da yakinin mutanen Anambra zasu amshi APC hannu 2
  • Gwamnan yace zai iyakar bakin kokarinsa ya ga cewa APC ta samu nasara a zaɓen gwamna dake tafe a jihar
  • A cewarsa wannan wata dama ce ga mutanen Anambra da zai zama wani ɓangare na jam'iyyar dake mulkin kasa

Anambra - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya yi ikirarin cewa babu ko tantama jam'iyyarsa ta APC ce zata lashe zaɓen gwamnan Anambra 2021.

Gwamnan wanda yake jagorantar kwamitin yakin neman zaɓe, yace farin jinin APC da nasarorin da ta cimmawa kaɗai sun isa su janye hankalin mutanen Anambra yayin kaɗa kuri'a.

Uzodinma ya faɗi haka ne yayin tattaunawa da Channels TV a cikin shirin 'Politics Today' ranar Talata.

Kara karanta wannan

Bidiyo ya bayyana yayin da APC ke rabawa gwamnoni manyan mukamai

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo
Jam'iyyar APC Ce Zata Lashe Zaben Gwamnan Anambra Dake Tafe, Uzodinma Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamnan yace:

"Zamu je tallata hajar mu, wadda kowa yake mararin sayenta cikin sauki, ina tunanin APC ce zata lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra a watan Nuwanba dake tafe 2021."

Ya kaji da nauyin da APC ta dora maka?

Da yake jawabi game da aikin da jam'iyyar APC ta ɗora masa, Uzodinma ya bayyana cewa zai yi iyakar bakin kokarin shi ya ga mutanen Anambra sun amince da kudirin APC.

Ya kara da cewa duk da sanin cewa jam'iyyar APGA ce ke mulkin jihar Anambra, amma APC ta wuce yadda ake tsammaninta.

Gwamnan yace jam'iyyar APC ta yi suna kuma ta zarce kowace jam'iyyar ƙasar nan wajen aiki tukuru.

Mutanen Anambra sun kosa su fita zabe

A cewar gwamnan, sakon da za'a isarwa mutanen Anambra game da APC zai sa su ƙagu lokaci yayi domin su zaɓi jam'iyyar da zata kawo musu cigaba har cikin gidansu.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

Gwamna Uzodinma yace APC zata baiwa al'ummar Anambra damar zama ɓangaren jam'iyyar dake jagorancin siyasa a ƙasar nan.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Saka Ranar Gangamin Tarukanta Na Kananan Hukumomi

Jam'iyyar APC mai mulki ta sanya ranar 4 ga watan Satumba domin gudanar da gangamin tarukanta na jihohi, kamar yadda punch ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da APC ta fitar ranar Laraba a Abuja ɗauke da sa hannun sakarenta.

A kwanakin bayane APC ta gudanar da zabukan shugabanninta a matakin gunduma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel