Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Tsohon Sakataren NMA, Sun Nemi a Tattaro Musu Kudin Fansa

Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Tsohon Sakataren NMA, Sun Nemi a Tattaro Musu Kudin Fansa

  • Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da ɗan tsohon sakataren kungiyar NMA
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace Adedamola Alayaki, a gonar mahaifinsa ranar Laraba
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Ogun ta tabbatar da faruwar lamarin, tace a halin yanzun jami'anta sun fara bincike

Ogun - Yan bindiga sun sace ɗan tsohon sakataren kungiyar likitoci ta kasa (NMA), Dr. Adewunmi Alayaki, a jihar Ogun, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Yan bindigan da suka sace ɗan sakataren, Adedamola Alayaki, sun nemi a tattara musu kuɗin fansa miliyan N20m kafin su sake shi.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa an yi awon gaba da ɗan tsohon sakataren ne a gidan gonar mahaifinsa dake yankin Isaga-Orile, karamar hukumar Abeokuta ta arewa, jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An Shiga Tashin Hankali a Wata Jami'a Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Dalibin 400 Level

Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Tsohon Sakataren NMA
Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Tsohon Sakataren NMA, Sun Nemi a Tattaho Musu Kudin Fansa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yan sanda sun kaddamar da bincike

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga mannema labarai ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bayanin Oyeyemi, Adedamola shine shugaban ɗaya daga cikin gidan gonan mahaifinsa.

Kakakin yan sandan ya tabbatar wa manema labarai cewa jami'an hukumar yan sanda na kan gudanar da bincike don kamo masu garkuwan.

Yace:

"Mun matsa sosai kan lamarin, kuma jami'an mu na kan bincike don gano waɗanda suka sace shi."

Channels tv ta ruwaito cewa lamarin satar mutane domin neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya.

Sai dai wannan sace ɗan tsohon sakataren NMA da ya faru ranar Laraba shine na baya-bayan nan a jihohin kudu maso yammacin kasar nan.

A wani labarin kuma An Shiga Tashin Hankali a Jami'a Jihar Ribas Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Dalibin 400 Level

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11, Sun Yi Awon Gaba da Wasu Sama da 40 a Jihar Zamfara

Dalibin da aka kashe, wanda har yanzun ba'a gano asalin sunanshi ba, an tabbatar da yana karatun injiniya ne a jami'ar.

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe ɗalibin ne a haraban ginin tsangayar kimiyya, inda ya fita shakatawa da abokansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel