Bayan wata da watanni babu haske a Maiduguri, NNPC za su samar da 50mw na lantarki
NNPC da wasu kamfanoni za su samar da wutar lantarki na gaggawa a Maiduguri
Mutanen garin Maiduguri da kewaye sun dade suna fama da matsalar rashin wuta
CMEC da GE za su bada gudumuwa a kafa tashar lantarki ta musamman a Borno
Kamfanin man fetur na kasa, NNPC, da wasu kamfanoni sun sa hannu domin samar da wutar lantarki na gaggawa a fadin garin Maiduguri, jihar Borno.
NNPC da kamfanin CMEC na China Machinery Engineering da General Electric (GE), sun kulla yarjejeniyar EPC domin kawo aikin kayan gyaran wutan.
The Cable ta ce kamfanonin za su samar da megawatt 50 na karfin wutar lantarki cikin gaggawa.
A wata sanarwa da NNPC ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, ta tabbatar da cewa an kulla yarjejeniyar wannan kwangila.

Kara karanta wannan
Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, NNPC ta ce aikin gyaran wutan na Maiduguri zai inganta kokarin da ake yi na cin moriyar karfin gas a fadin Najeriya.
“Aikin zai taimaka wajen yaye kalubalen rashin wutar lantarki da ake fama da shi a babban birnin jihar Borno.”

Asali: UGC
A watan Afrilun 2021, shugaban NNPC na kasa, Mele Kolo Kyari, ya yi alkawarin za su yi maganin matsalar da mutanen Maiduguri da kewaye suke fuskanta.
“Muna tunanin zai yiwu a samar da tashar wutar lantarki a Maiduguri wanda zai magance matsalolin da ake fama da su, kuma ya kai wuta zuwa garuruwan kewaye, har zuwa wasu kasashe.”
Cikin kankanin lokaci, nan da watanni uku zuwa hudu ake sa ran za a kammala wannan aikin.
Idan aka cin ma nasarar wannan aiki, al’umma za su samu wutar lantarki nan da karshen shekara. Matsalar ta jawo abubuwa sun kara tsada a Maiduguri.
An sake kai hari a Filato
Rahotanni sun ce takunkumin hana zirga-zirga da gwamnatin jihar Filato ta sa bai hana kashe-kashen mutane ba, bayan abin da ya faru a hanyar Jos kwanaki.
‘Yan bindiga sun sake kashe mutane biyar, sannan an nemi akalla mutane hudu an rasa a garin Bassa.
Asali: Legit.ng