Duk da an kafa dokar hana fita, miyagu sun yi mamaya, an sake hallaka mutane a Jihar Filato
- ‘Yan kabilar Irigwe sun ce an kai masu hare-hare, an hallaka mutane biyar a Bassa
- Shugaban kungiyar mutanen Irigwe yace an kashe masu mutane cikin lokacin kulle
- Wasu Bayin Allah sun bace bayan harin da aka kai a kauyukan Dong da Tafi-Gana
Jos - ‘Yan bindiga sun kuma kai wani danyen hari a karamar hukumar Bassa, Filato, a lokacin da gwamnati ta bada umarnin kowa ya zauna a gida.
An auka wa mutanen Dong, Tafi-Gana
Jaridar This Day ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 19 ga watan Agusta, 2021, ta ce an hallaka mutane akalla biyar a sabon hare-haren da aka kai.
An kai harin ne a lokacin da ba a gama makokin wasu matafiya da aka kashe a hanyar Jos ba.
Wadanda suka yi wannan ta’adi sun auka wa kauyen Tafi-Gana cikin dare a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, a lokacin da mutane suke barci.
Haka zalika ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Dong, a nan ma an hallaka mutum daya kamar yadda wani dattijo, Danjuma Auta, ya fada wa ‘yan jarida.
Da yake magana a ranar Laraba, shugaban kungiyar Irigwe Development Association, Mista Ezekiel Bini, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.
Ezekiel Bini yace an kashe mutum biyar, kuma an nemi mutane hudu an rasa inda suka shiga bayan ta’adin.
“Gaskiya ne an kashe mutane biyar a danyen harin da aka kawo mana. Yanzu haka za mu je mu gana da gwamna kan kashe-kashen da ake yi a Bassa.”
Su wanene su ka yi wannan aika-aika?
Rahoton yace ana zargin makiyaya ne suka yi wannan danyen aiki a garin Bassa, sai dai kuma babu wata hujja da za ta iya gaskata zargin da ake yi.
Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, watau MACBAN, tace babu hannunta a sabon harin da aka kai.
Da take maida martani, Kungiyar Miyetti Allah ta kasa, tace bai kamata a rika alakanta kowane mummunan hari irin wannan da Fulani a Filato ba.
Kisan matafiya kusan 40
Bayan an hallaka fasinjoji da-dama a hanyar Jos, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnati ta hukunta wadanda ke da hannu a laifin.
"Za mu dauki dukkan matakai da shari’a ta yadda da su. Muna kira ga musulmai, muna bada hakuri cewa ka da mu dauki wani mataki a hannunmu.”
Asali: Legit.ng