Hankalin ISWAP ya tashi, sun sauya tsarin shugabanci yayin da Boko Haram ke tuba

Hankalin ISWAP ya tashi, sun sauya tsarin shugabanci yayin da Boko Haram ke tuba

  • Mayakan ISWAP sun canja shugabanninsu da masu basu shawara sakamakon yadda mayakan Boko Haram da dama suka yada makamansu
  • Rahotanni sun bayyana yadda tun daga hedkwatar kungiyar ta ISIS suka bayar da umarnin canja shugabannin
  • Hakan ya biyo bayan rabuwar kawunan mayakan tun bayan mutuwa shugabansu, Abubakar Shekau

Borno - Mayakan ISWAP na Najeriya sun canja tsarin shugabancinsu da kungiyar masu basu shawarwari akan yadda mayakan Boko Haram da dama suka zubar da makamansu ga sojojin Najeriya.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, an tumbuke shugabannin ne bisa umarnin hedkwatar ISIS na Iraq da Syria, bisa kasa tabbatar da hadin kan ISWAP da mayakan Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Shekau.

Hankalin ISWAP ya tashi, sun sauya tsarin shugabanci yayin da Boko Haram ke tuba
Hankalin ISWAP ya tashi, sun sauya tsarin shugabanci yayin da Boko Haram ke tuba. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Sabon tsarin shugabancin

Aba-Ibrahim ne ya maye gurbin Abbah-Gana wanda aka dauka a matsayin shugaban ISWAP, sai Malam Bako, Abdul-Kaka wanda aka fi sani da Sa’ad, Abu Ayun da Abba Kaka, su ne sababbin wadanda aka dauka a kungiyar masu bayar da shawara na ISWAP.

Kara karanta wannan

DHQ: Shugabannin Kungiyar ISWAP sun gigice, ganin Boko Haram suna ta ajiye kayan yaki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran wadanda aka nada a mukamaimanya sun hada da Muhammed Mustapha wanda shine shugaban Marte, Muhammed Malunma, Muhammad Maina da Abubakar Dan-Buduma wadanda suka maye gurbin tsofaffin kwamandoji.

Hakan yana nuna cewa suna da manufar dakatar da duk wasu da suke son yin murabus da zubar da makamansu.

Bayanin masana harkokin ta'addanci

Majiyoyi masu ilimi akan harkokin ‘yan ta’addan sun tabbatar wa da PRNigeria cewa an matsawa ISWAP ta canja tsarin mulkinta sakamakon yadda mayakan suke ta tuba.

Yanda daruruwan mayakan suka yi ta zubar da makamansu ya kawo damuwa da tashin hankali a sansanayen ISWAP dake Kirta, Wulgo, Sabon Tumbu, Jubularam, Kwalaram, Sigir, Kayowa da Kurnawa inda akwai mayaka da dama da basu da yadda zasu yi idan basu mika wuya ba sai dai su fada tafkin Chadi.

Majiyar ta tabbatar wa da PRNigeria cewa bama-bamai da ragargaza a wurare daban-daban ya janyo ‘yan ta’addan suna boyewa wuri-wuri sakamakon hakan yunwa da wahalar rayuwa ta riski sansanayensu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka yan ta'addan IPOB 6, an damke 13, an kwace AK47 guda 19

An kama mayakan JAS da dama kuma duk an kwamushesu a gidan yarin ISWAP dake Tumbun Kayowa sakamakon laifuka da dama kuma an ragewa manyan kwamandojin matsayi inda suka koma kananun mayaka kuma kamar bayi a sansanin ISWAP.

Sojin saman Najeriya sun sheke shugabannin 'yan bindiga 3 a dajin Kuyambana dake Zamfara

A wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya sun yi nasarar sheke shugabannin 'yan bindiga 3 tare da wasu miyagu a dajin Kuyambana dake jihar Zamfara.

Cigaban ruwan wutan da ake yi wa miyagun 'yan bindigan ya janyo ajalin shugabannin 'yan bindigan da suke ta'addaci a jihar Zamfara, PRNigeria ta ruwaito.

Kamar yadda wani jami'in sirri da aka yi ragargaza ta jiragen yakin tare da shi ya sanar, yace an sheke shugabannin 'yan bindigan a dajin Kuyambana, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel