Da Dumi-Dumi: An Shiga Tashin Hankali a Wata Jami'a Yayin da Yan Bindiga Suk Hallaka Dalibin 400
- Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun harbe ɗalibin jami'ar jihar Ribas har lahira da safiyar Alhamis
- Rahotanni sun bayyana cewa an kama wani ɗalibi ɗan aji 2 da hannu a lamarin kisan
- Hukumar yan sanda ta tabbatar da kisan ɗalibin, tace yanzun haka ana kan bincike don kamo yan bindigan
Rivers - An shiga yanayin tashin hankali a jami'ar jihar Ribas (RSU) yayin da wasu yan bindiga suka harbe ɗalibin makarantar har lahira, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Dalibin da aka kashe, wanda har yanzun ba'a gano asalin sunanshi ba, an tabbatar da yana karatun injiniya ne a jami'ar.
Rahotanni sun bayyana cewa an harbe ɗalibin ne a haraban ginin tsangayar kimiyya, inda ya fita shakatawa da abokansa.
Su wa ake zargi da aikata kisan?
Wata majiya da ya bayyana sunansa da Emmanuel, yace ana zargin ɗalibin aji 2 da hannu a kisan mamacin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Emmanuel yace an harbi dalibin ne a tsakiyar kansa, kuma lamarin ya faru da misalin karfe 9:00 na safiyar Alhamis.
Ya kara da cewa makasan ɗalibin sun tsere daga wurin kafin daga bisani jami'an tsaro suka cafke ɗalibin aji 2 da zargin yana da hannu a lamarin.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar ranar Alhamis.
Omoni yace:
"Ina tabbatar da faruwar lamarin a jami'ar jihar Ribas da safiyar nan. Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin sun aikata kisan ya shiga hannu."
"Kwamishinan yan sanda ya kaddamar da binciken kamo waɗanda suka aikata kisan kuma ba da jimawa ba zasu shiga hannu."
"A halin yanzun an samu kwanciyar hankali a jami'ar, mun dawo da zaman lafiya a cikin makarantar."
A wani labarin kuma ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, ya bayyana dalilim da yasa shugaba Buhari ke zuwa Landan neman lafiya
Ministan yaɗa labaru da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace fita kasar waje duba lafiya da shugaba Buhari ke yi ba yana nufin ɓangaren lafiya a Najeriya ya lalace bane.
Ministan yace shugaban yana da damar zaɓan likitocin da zasu duba lafiyarsa domin ba shine na farko dake fita kasar waje ba.
Asali: Legit.ng