Luguden harbe-harben cikin dare yayi ajalin rayuka 5 a Cross River
- Harbe-harbe sun tsananta a daren Talata a wasu unguwanni biyu na wurin Yala dake jihar Cross River
- Kamar yadda rohotanni suka tabbatar, an ga gawar mutane 5 kuma har yanzu harbe-harben basu tsaya ba
- Kwamishinan ‘yan sandar jihar ya tabbatar da aika jami’ansa yankin don kwantar da tarzomar
Yala, Cross River - Da daren Talata ne aka fara jin harbe-harbe ko ta ina a wasu unguwanni biyu dake wuraren Yala a jihar Cross River.
Anji harbin ne a O’oba da Okpame tun cikin dare har yanzu haka ba a daina ji ba kamar yadda wakilin Daily Trust na jihar yace.
Kwamishinan 'yan sandan jihar ya dauka mataki
Kwamishinan ‘yan sanda na Cross River ya tabbatar da tura jami’ansa da yayi yankin don kwantar da tarzoma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasu bata-gari daga O’Oba sun afka wasu anguwannin suna harbe-harbe, a cewarsa.
Ina sane da abubuwan da suke faruwa don haka ne yasa na tura yarana yankin.
Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai gidajen da aka bankawa wuta. Daya daga cikin gidajen na Gabe Onah ne, tsohon shugaban CRCC.
Yanzu haka ba a riga an tantance yawan asarorin da aka tafka ba. Amma an tsinci gawar mutane 5 da aka harbe har lahira.
Gwamnatin tarayya zata ci bashin N4.89trn don daukar nauyin kasafin 2022
Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirinta na amso rancen cikin gida da na waje na naira tiriliyan 4.89 don samar da kudaden kasafin shekarar 2022 na naira tiriliyan 5.62.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Ministar kudi ta bayyana wannan kudirin a wata takarda da ta mika ga ma’aikatarta ne ga majalisar wakilai ta MTEF da FSP na 2022 zuwa 2024 a ranar Litinin.
Ministar ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, a gabatarwar da tayi ta ce gwamnatin tarayya za ta rage yawan kudaden da take narkawa ma’aikatu, sasanni da hukumomi da naira biliyan 259.31.
Ta bayyana yadda gibin da za a isa dashi 2022 na naira tiriliyan 5.62 ya karu fiye da naira tiriliyan 5.60 a 2021, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng