'Batanci: Gwamnatin Kano Ta Ɗauki Manyan Lauyoyi 4 Masu Muƙamin SAN Don Shari'ar Abduljabbar

'Batanci: Gwamnatin Kano Ta Ɗauki Manyan Lauyoyi 4 Masu Muƙamin SAN Don Shari'ar Abduljabbar

  • Gwamnatin Jihar Kano ta dauki sabbin manyan lauyoyi hudu masu mukamin SAN domin shari'ar Sheikh Abduljabbar
  • Manyan lauyoyin hudu sun hallarci zaman kotun na ranar Laraba inda suka nemi a janye tsohuwar tuhumar da ake yi wa Abduljabbar a maye gurbinta da sabuwa
  • Amma lauya mai kare Abduljabbar, Saleh Muhammad Bakaro, ya ce SAN din ba su da ikon kare kowa a kotun shari'a sannan janye tuhuma da niyyar maye gurbinsa da sabuwa ta sabawa doka a karkashin shari'ar musulunci

Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta dauki manyan lauyoyi masu mukamin SAN guda hudu domin gurfanar da malamin addinin musulunci na jihar, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan ya faru ne a yayin da kotun ta cigaba da sauraron shari'ar malamin a ranar Laraba a babban kotun shari'ah da ke zamanta a Kofar Kudu a birnin Kano karkashin jagorancin Mai Shari'a Abdullahi Sarki Yola.

Kara karanta wannan

Hujjojin da Aka Kawo Sun Mun Tsauri, Alkalin Kotu Ya Dage Sauraron Karar Sheikh Abduljabbar

'Batanci: Gwamnatin Kano Ta Ɗauki Manyan Lauyoyi 4 Masu Muƙamin SAN Don Shari'ar Abduljabbar
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar rahoton na Daily Trust, Gwamnain Kano ta fara gurfanar da Sheikh Kabara ne a kotun a ranar 16 ga watan Yuli sakamakon wani rahoto na FIR mai alaka da batanci, tada zaune tsaye da wasu laifukan.

Sabuwar bukata da lauyoyin na SAN suka gabatarwa kotu?

A yayin zaman kotun a ranar Laraba, jagoran lauyoyin, Suraj Sa'eda, SAN, ya bukaci kotun ta yi watsi da karar na FIR na farko sannan suka gabatar da sabon tuhuma mai dauke da kwanan watan ranar 13 ga watan Agusta.

Sa'eda ya ce ya zama dole a karanto tuhumar a kuma saurara kafin a bawa mai kare kansa dama ya ce wai abu kamar yadda sashi na 390(2) na dokar masu laifi na jihar Kano na 2019 ya tanada.

Mene Lauyan Abduljabbar ya ce game da daukan SAN guda hudu?

Kara karanta wannan

Abduljabbar ya rame: Sheikh Abduljabbar ya sake gurfana a gaban kuliya

Lauyen wanda ake kara, Mr Saleh Muhammad Bakaro, ya shaidawa kotu cewa lauyoyin hudu SAN da ke wakiltan Atoni Janar na Jihar Kano ba su da hurumin kare kowa a kotun Shari'ar na Kano.

Ya ce:

"Lauyoyi masu mukamin SAN ba su da hurumin kare kowa a babban kotun shari'a.
"Sashi na 3,4,5 da 6 (3) sun fayyace alfarma da ayyukan SAN."

Muhammad Bakaro ya kuma roki kotun kada ta bada ikon a sake gabatar da sabbin tuhuma kan wanda ake kara, yana mai cewa a karkashin shari'ar musulunci ba bu ikon a sauya tuhuma bayan an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu a cewar sashi na 2, 108 da 126(a) na shari'ar masu laifi na 2019.

Kotun ta tsayar da ranar 2 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan bukatar da aka nema na sake shigar da sabuwar kara kan wanda ake tuhumar.

Alkalin ya kuma bada umurnin a cigaba da tsare wanda ake tuhumar a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Sheikh Abduljabbar ya sake gurfana a gaban kuliya

A wani labari mai alaka da wannan, rahoto ya bayyana cewa, an sake kai Malam Abduljabbar Nasir Kabara gaban kotu a bisa tuhumarsa da yin kalaman tunzura jama'a da batanci ga Annabi SAW.

Zargin da Malamin ya musanta a baya. Legit Hausa ta tattaro muku, a ranar 30 ga watan Yulin da ta gabata aka fara shari'ar Abduljabbar Nasir Kabara, inda aka gabatar da takardar korafi a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel