Abduljabbar ya rame: Sheikh Abduljabbar ya sake gurfana a gaban kuliya

Abduljabbar ya rame: Sheikh Abduljabbar ya sake gurfana a gaban kuliya

  • A karo na biyu, an sake kawo Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara gaban kotu domin daddale laifukansa
  • A halin yanzu an tsaurara tsaro fiye da zaman kotu na farko, kuma rahoto ya ce Malamin ya rame sosai
  • An zauna zaman kotu a watan jiya, inda aka dage karar zuwa yau 18 ga watan Agusta don ci gaba

Kano - Rahoto ya bayyana cewa, an sake kai Malam Abduljabbar Nasir Kabara gaban kotu a bisa tuhumarsa da yin kalaman tunzura jama'a da batanci ga Annabi SAW. Zargin da Malamin ya musanta a baya.

Legit Hausa ta tattaro muku, a ranar 30 ga watan Yulin da ta gabata aka fara shari'ar Abduljabbar Nasir Kabara, inda aka gabatar da takardar korafi a kansa.

A karo na biyu: Sheikh Abduljabbar ya sake gurfana a gaban kuliya
Malam Abduljabbar Nasiru Kabara | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

A cewar gwamnati, an gurfanar da Malamin Abduljabbar, bisa kaurin suna da ya yi wajen yin wa'azin da ke haifar da mahawara da kuma zargin furta kalaman batanci ga Annabin SAW.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

A cewar wakilin BBC da ke cikin kotun da ake sauraren karar ya ce an tsaurara tsaro fiye da zaman kotun da aka yi a farko.

Ya kuma ce Malam Abduljabbar ya rame ba kamar yadda ya bayyana a sauraran kararsa da ake yi a kotun a watan jiya ba.

Yadda zaman kotu ta kaya a shari'ar Abduljabbar a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Malami, Sheikh AbdulJabbar Nasir Kabara gaban kotun Shari'ar Musulunci a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, 2021.

Wannan ya biyo bayan damkeshi da hukumar yan sanda tayi gabanin bikin Sallar Layya a ranar 17 ga Yuli, 2021.

A wancan lokacin, an ci gaba da sauraran abubuwan dake faruwa daga kotun.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin a shiga da Sheikh Albduljabbar cikin akwatin wanda ake kara ke tsayawa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Kuma, Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano.

Batun Abba Kyari: Kwamiti ya gama bincike, ya mika rahoto ga Sufeto-Janar

A wani labarin, Kwamitin Bincike na Musamman ya mika rahotonsa ga Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba, makonni biyu bayan da aka umarce shi da ya binciki tsohon Shugaban rundunar IRT kuma Mataimakin Kwamishinan' Yan sanda, Abba Kyari.

Kwamitin na mutum hudu karkashin jagorancin Mataimakin Sufeto -Janar na 'yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar, Joseph Egbunike, ya mika sakamakon binciken ga IG ranar Litinin 16 ga watan Agusta.

A baya mun rahoto cewa, hukumar FBI ta kasar Amurka ta zargi Abba Kyari da hannu cikin wata damfara da Abbas Ramon (Hushpuppi) ya yi kan wani dan kasuwar Qatar, Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel