'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi awon gaba da kayan abinci a Abuja

'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi awon gaba da kayan abinci a Abuja

  • Masu garkuwa da mutane sun harbe wani matashi, Haruna Dako har lahira kuma sun saci kayan abinci
  • Lamarin ya faru ne a Kambu dake wuraren Abaji a Abuja a ranar Juma’a da misalin karfe 10:27pm na dare
  • Dako ya je shago ne ya kai cajin wayarsa sai suka yi arangama dasu, ya yi kokarin tserewa ne suka harbe shi

FCT, Abuja - Masu garkuwa da mutane sun harbe wani matashi, Haruna Dako, sannan sun sace kayan abinci iri-iri a Kambu dake wuraren Abaji a birnin tarayya, Abuja.

Daily Trust ta ruwaito yadda kauyen Kambu, wanda yake karkashin Chakumi yakeda iyaka da Gwagwalada, inda Rafin Gurara yake gudana tsakanin garuruwan.

'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi awon gaba da kayan abinci a Abuja
'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi awon gaba da kayan abinci a Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya kasance

Mazaunin garin mai suna Yahaya ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 10:27 na dare lokacin da masu garkuwa da mutane suka shigo garin da yawansu.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Marigayin ya fito daga gidansa ne ya kai cajin wayarsa wani shago, kwatsam masu garkuwa da mutanen suka tsare shi.

Ya je bayar da wayarsa caji ne a wani shago yana hanyar komawa gida ya gamu da daya daga cikin ‘yan bindigan wanda ya umarce shi da ya tsaya.
Saboda tsabar tsoro yayi kokarin tserewa aikuwa dan bindigan ya harbe shi take anan ya mutu, a cewarsa.

A cewar mutumin, masu garkuwa da mutane sun umarci kowa da ya kwanta kafin suka kwashe kayan abinci kamar shinkafa, wake da indomi kafin suka bar kauyen.

A cewarsa iyalan mamacin sun birne gawarsa, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin hukumar ‘yan sanda, ASP Mariam Yusuf bata daga wayar wakilinmu ba kuma bata bayar da amsar sakon da tace ya tura mata ba.

Nasara: Bidiyon 'yan ISWAP-Boko Haram na tururuwar tuba a Mafa dake Borno

Kara karanta wannan

Gada ta ruguje a Jigawa, ta hallaka matafiya ciki har da masu neman aikin soja

A halin yanzu, dakarun sojin Najeriya sun karba kwamandoji da mambobin Boko Haram da suka tuba sama da 1,500 a gagarumar tururuwar da tsoffin 'yan ta'addan ke yi wurin tuba.

A wani bidiyo da PRNigeria ta samu, an ga tubabbun 'yan ta'adda masu tarin yawa, iyalansu da suka hada da mata tare da kananan yara, suna fitowa a dogon layi daga dajikan yankin.

Wadanda ke fitowa daga dajikan sun gangara gaban sojoji dake Mafa, daga baya aka gano. Wasu daga cikin manyan kwamandojin kungiyar, da suka hada da Adamu Rugurugu da iyalansa sun mika wuya ga sojojin a wurare daban-daban dake jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel