Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 4, Sun Yi Awon Gaba da Wasu da Dama a Katsina

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 4, Sun Yi Awon Gaba da Wasu da Dama a Katsina

  • Miyagun yan bindiga sun kai hari Kauyen Tsayau, karamar hukumar Jibiya da daren ranar Litinin
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe aƙalla mutum 4 tare da jikkata wasu 7 yayin harin
  • Mazauna ƙauyen sun koka matuka kan yadda miyagun suka ɗauki tsawon lokaci suna ta'adi ba tare da an kawo ɗauki ba

Katsina - Wasu yan bindiga sun sheke aƙalla mutum 4 a kauyen Tsayau, karamar hukumar Jibiya, jihar Katsina, ranar Litinin.

Dan majalisa mai wakiltar Jibiya a majalisar dokokin jihar shine ya tabbatar da haka ga Premium times.

Yace yan bindigan sun jikkata wasu mutum 7 tare da yin awon gaba da wasu da dama a yayin da suka kai mummunan harin.

Wasu yan bindiga sun kai hari jihar Katsina
Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 4, Sun Yi Awon Gaba da Wasu da Dama a Katsina Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yaushe aka kai harin?

Kara karanta wannan

Da Dumi-Duminsa: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kaduna

Wata majiya daga yankin da lamarin ya faru ta bayyana cewa maharan sun farmaki garin ne da misalin karfe 7:30 na dare ɗauke da muggan makamai.

Majiyar tace:

"Maharan sun shigo da misalin karfe 7:30 na dare ɗauke da manyan bindigu. Daga isar su suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, a wannan lokaci ne suka bindige mutum 4."

Mazauna ƙauyen sun bayyana sunayen waɗanda aka kashe da suka haɗa da, Umma Ta-malam, Jamilu Ibrahim, Amira Ibrahim, da kuma Zainab Wada.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Majiyar ta kara da cewa sai bayan miyagun sun gama aikata ta'adin sun fece sannan jami'an tsaro suka kariso kauyen.

Mazauna Ƙauyen sun koka kan yadda maharan suka ci karansu babu babbaka na tsawon awa ɗaya ba tare da an kawo ɗauki ba duk kuwa da kiran gaggawa da suka yi wa sojojin Gurbi, tafiyar Kilomita ɗaya zuwa Tsayau.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Malamai da Dalibin Kwalejin Zamfara Sun tsero Daga Hannun Yan bindiga

A wani labarin kuma Barayin da Suka Sace Malamai, Dalibai a Kwalejin Zamfara Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N350m

Yan bindigan da suka sace malamai da ɗalibai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura, jihar Zamfara, sun nemi a basu miliyan N350m kuɗin fansa.

Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntuɓe shi ta wayar salula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262