2023: Cancanta ya kamata a bi wajen zabar wanda zai zama Shugaban Najeriya, in ji Yahaya Bello
- Gwamna Yahaya Bello ya ci gaba da kamfen dinsa na adawa da mulkin karba-karba gabanin zaben 2023
- Gwamnan na Kogi wanda tun da farko ya nuna sha’awar tsayawa takara ya ce cancanta ya kamata a fi ba mahimmancin wajen hawa kujerar
- Gwamnan ya nanata matsayinsa a wani taron da kungiyar Matasan Najeriya ta gudanar a Lafia
Lafia - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce cancanta ne ya kamata ya zama babban abin da 'yan Najeriya za su fi mayar da hankali a kai, domin su ne za su zabi shugaban kasar na gaba a 2023, jaridar Punch ta ruwaito.
Bello ya fadi hakan ne a jawabin da babban hadiminsa, Mohammed Abdulkareem ya yi a madadinsa a yayin wani taro a jihar Nasarawa a ranar Talata, 17 ga watan Agusta.
"Ya zama dole zaɓin wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba a 2023 ya dogara kan wanda ya dace ba wai a kan yankin da ya fito ba."
A halin da ake ciki, jaridar Premium Times ta rahoto cewa Nigerian Indigenous Nationalities Alliance for Self-Determination ta ce babu wani zabe da za a yi a Najeriya a shekarar 2023 sai dai idan gwamnatin tarayya ta amince ta gudanar da kuri'ar raba gardama ga dukkan kungiyoyin da ke cin gashin kansu a kasar.
Shugaban kungiyar, Banji Akintoye, ya ce idan aka dakatar da zaben 2023 a shekarar 2021, Kundin Tsarin Mulkin 1999 zai ba da damar gudanar da zaben raba gardama na yanki don cin gashin kai.
Ya kara da cewa ya kamata a dauki matakin dakatar da shirye -shiryen zuwa babban zaben 2023 cikin gaggawa.
A wani labarin, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tana shirye-shiryen gaske don samun nasara yayin zaben gwamnan Anambra mai zuwa.
Daya daga cikin irin wannan shirye-shiryen shine kaddamar da kwamitin yakin neman zabe wanda ya kunshi galibin shugabannin jihohi kamar Gwamna Hope Uzodinma, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da Gwamna Yahaya Bello.
Asali: Legit.ng