Bidiyo ya bayyana yayin da APC ke rabawa gwamnoni manyan mukamai
- Jam’iyyar APC mai mulki bata shirya barin wata kafa gabannin zaben gwamnan Anambra
- Domin tabbatar da ganin cewa ta kwace jihar ta kudu maso gabas, jam’iyya mai mulki ta fara yin manyan tsare-tsare a cikinta
- Kwamitin rikon kwarya na Gwamna Buni a ranar Talata, 17 ga watan Agusta ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabe wanda Gwamna Hope Uzodinma zai jagoranta
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tana shirye-shiryen gaske don samun nasara yayin zaben gwamnan Anambra mai zuwa.
Daya daga cikin irin wannan shirye-shiryen shine kaddamar da kwamitin yakin neman zabe wanda ya kunshi galibin shugabannin jihohi kamar Gwamna Hope Uzodinma, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da Gwamna Yahaya Bello.
Wani babban jigon APC wanda ya kasance mamba a kwamitin shine mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, Daily Trust ta rahoto.
Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar mai mulki, Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ne ya kafa kungiyar a Abuja a ranar Talata, 17 ga watan Agusta.
Da yake kaddamar da kwamitin, Buni ya bayyana cewa an zabi mambobin ne bisa iyawarsu da kuma tabbacin za su yi aiki tare don kawo jihar a zaben.
Buni ya bayyana fatan cewa a karkashin jagorancin Gwamna Uzodinma, kungiyar za ta fito da gagarumar nasara a aikin ta.
Kalamansa:
"An zabi mambobin kwamitin a hankali saboda karfin ku daban-daban da imanin cewa, a matsayin ku na kwamiti, za ku kawowa jam’iyyar jihar.
"An umarce ku da yin aiki tare a matsayin tawaga sannan kuma ku ɗauki kowa da kowa a cikin tafiyar. An kuma shawarce ku da ku daidaita sabanin da ke tsakanin membobin jam'iyyar wanda wataƙila ya taso bayan zaɓen fidda gwani na gwamna, domin mu tunkari zaɓen tare da haɗin kai.
"Ba na shakka wannan kwamiti mai karfi karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Hope Izoduma na jihar Imo, zai sa mu alfahari da kama jihar Anambra zuwa APC."
A wani labarin, gabanin babban zaben shekarar 2023, wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Ribas, Cif Tony Okocha, ya yi wasu hasashe marasa kyau ga jam'iyyar mai mulki.
A ganin Okocha, lashe zaben shugaban kasa mai zuwa zai kasance babban aiki ga APC saboda 'yan Najeriya sun rasa karfin gwiwa kan ta.
Ya ce jam'iyyar da ta hau mulki tare da alƙawarin canza mummunan halin da ake zargin mulkin shekaru 16 na jam'iyyar PDP ya kawo ba ta samu wani ci gaba mai ma'ana ba ta fuskar tattalin arziki, kayayyakin more rayuwa, isar da lafiya, da samar da ayyukan yi.
Asali: Legit.ng