Hayakin janareto ya hallaka mutane 7 'yan gida daya a jihar Osun
- Wasu iyalai sun mutu sanadiyyar hayakin janareto a wani yankin Osun a kudancin Najeriya
- Rahoton 'yan sanda ya bayyana haka, amma ana ci gaba da bincike don gano gaskiyar hakan
- An kuma samu nasarar ceto wata yarinya 'yar shekaru 14 daga cikin gidan da abin ya faru
Osun - An tsinci gawar wasu mutane bakwai 'yan gida daya a cikin dakunansu a karamar hukumar Apomu ta jihar Osun, ranar Talata 17 ga watan Agusta.
Rundunar 'yan sandan Osun ta ce ana zargin hayaki daga janareto ne sanadin mutuwarsu, amma sakamakon binciken gawa zai tabbatar da musabbabin mutuwar tasu.
Yemisi Opalola, mai magana da yawun rundunar, ta ce akwai mutane takwas a dakuna daban-daban na gidan amma mutum daya ne kawai aka tarar yana numfashi.
Ta ce an sama janareto a cikin gidan kuma rahoto na cewa dangin sun yi amfani da janareto a ranar da ta gabata, lamarin da yasa ake zargin gubana carbon monoxide ne ya kashe su, amma ana ci gaba da bincike don gano ainihin batun.
A cewarta:
"Za a gudanar da bincike kan gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su don gano hakikanin musabbabin mutuwarsu."
An ceto wata yarinya 'yar shekara 14
Hakazalika, rahoton Premium Times ya ce an yi nasarar ceto wata yarinya 'yar shekaru 14, wacce aka samo a cikin daki kwance a sume.
A cewar Yesimi:
“Mutum daya, yarinya 'yar shekara 14, an same ta a raye (duk da cewa a sume) kuma an kai ta asibiti inda take samun sauki.
"An kuma kai gawarwakin sauran mamatan Asibitin Koyarwa na Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU), da ke Ile-Ife, inda za a yi musu bincike don gano musabbabin mutuwarsu".
Makwabta ne suka gano mamatan wadanda suke tunanin sun mutu yayin da suke barci..
Kafin haka,, rahoto yana cewa an kai gawarwakin zuwa wani asibiti mai zaman kansa a cikin unguwar, amma an ki karbar su kafin a kai su dakin ajiye gawarwaki na asibitin koyarwa na OAU.
Kisan Musulmai a Jos: Majalisar malamai ta ce kada Musulmai su dauki doka a hannu
A wani labarin, Majalisar Malamai/Dattawa ta Jihar Filato ta yi kira ga al’ummar Musulmi da ke Jos da kada su kai farmaki kan kowa don daukar fansa kan kisan da aka yi wa musulmai a kan hanyar Gada-biyu - Rukuba, cikin Karamar Hukumar Jos ta Jihar Filato.
An kashe wasu Fulani matafiya musulmai a ranar Asabar a kan hanyarsu ta komawa jihohin Ondo da Ekiti bayan sun halarci wani hidiman addini a Bauchi, an kai musu hari inda aka kashe sama da 20, mutane da yawa sun ji rauni kuma kusan 10 sun bace.
A rahoton Daily Trust, ta ce wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar, Ahmad Muhammad Ashir ya ce:
"Musulunci bai goyon bayan tashin hankali saboda haka bai kamata a kai hari ko kashe wani da sunan daukar fansa ba."
Asali: Legit.ng