Hajji 2021: Jihar Kano za ta mayar wa maniyyata aikin Hajji 2,300 kudadensu
- Jihar Kano ta yi kira ga maniyyata aikin Hajjin 2021 su zo su karbi kudaden da suka biya
- Wannan na zuwa ne watanni bayan gudanar da aikin Hajjin ba tare da karbar 'yan wata kasa ba
- Hukumar jin dadin Alhazai a jihar ta bayyana adadin mutanen da suka biya kudadensu na Hajji
Kano - Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano (KSPWB), ta ce za ta mayar wa maniyyata 2,300 da suka ajiye kudin aikin hajjin 2021 kudaden su.
Gwamnatin Saudiyya a ranar 12 ga watan Yuni, ta ba da sanarwar cewa alhazan kasashen waje ba za su samu damar yin aikin Hajjin 2021 ba, tare da takaita aikin hajjin ga 'yan kasar da mazauna cikinta.
Mahajjata 60,000 suka yi aikin Hajji a 2021 saboda cutar ta Korona, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Matakin jihar Kano game da maniyyata aikin Hajjin 2021
Babban Sakataren Hukumar ta KSPWB, Alhaji Muhammad Abba ya bayyana nufin mayar da kudaden ga maniyyata a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba 18 ga watan Agusta, 2021 a jihar Kano.
Legit Hausa ta tattaro daga News Diary in da Abba ya ce maniyyata 5,500 ne suka yi rajistar aikin Hajjin 2021 a jihar.
A cewarsa:
"Sama da ceki 200 a shirye amma masu su ba su zo ba, muna kuma sarrafa karin ceki din."
Abba ya yi kira ga sauran maniyyatan da ke son karbar kudinsu da su rubuto a rubuce, domin a ba da ceki kudinsu.
NAN ta ba da rahoton cewa a shekarar 2020, mahajjata 1,000 ne aka ba su izinin yin aikin hajji saboda Korona.
Abduljabbar ya rame: Sheikh Abduljabbar ya sake gurfana a gaban kuliya
A wani labarin, Rahoto ya bayyana cewa, an sake kai Malam Abduljabbar Nasir Kabara gaban kotu a bisa tuhumarsa da yin kalaman tunzura jama'a da batanci ga Annabi SAW. Zargin da Malamin ya musanta a baya.
Legit Hausa ta tattaro muku, a ranar 30 ga watan Yulin da ta gabata aka fara shari'ar Abduljabbar Nasir Kabara, inda aka gabatar da takardar korafi a kansa.
A cewar gwamnati, an gurfanar da Malamin Abduljabbar, bisa kaurin suna da ya yi wajen yin wa'azin da ke haifar da mahawara da kuma zargin furta kalaman batanci ga Annabin SAW.
Asali: Legit.ng