Goggo: Gwamnatin Jihar Kano ta musanya rade-radin cewa ‘Murtala Garo zai gaji Ganduje a 2023’

Goggo: Gwamnatin Jihar Kano ta musanya rade-radin cewa ‘Murtala Garo zai gaji Ganduje a 2023’

  • Gwamnatin Kano ta yi karin-haske a kan wasu kalaman Farfesa Hafsat Ganduje
  • Ana zargin Matar gwamnan tace Murtala Garo ne zai gaji kujerar Gwamna a 2023
  • Kwamishinan labarai, Muhammad Garba ya yi watsi da fassarar da aka yi mata

Kano - Mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa yana da ‘dan takarar da zai gaje shi.

Hakan na zuwa ne bayan wasu kalamai da ake cewa sun fito daga bakin mai dakinsa, inda ta ayyana ‘dan siyasar da ake tunanin zai zama gwamna.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace bai tsaida wani ‘dan siyasa da zai maye gurbinsa ba. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a farkon makon nan.

Gwamnan Kano bai da 'dan takara a 2023

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Buni, Bagudu, Abubakar sun hadu da Bankole a Abeokuta

A wani jawabi da gwamnatin jihar Kano ta fitar ta bakin kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ta ce gwamnan bai da ‘dan takara.

Malam Muhammad Garba ya na mai karin-bayani, yake cewa mutane sun juya kalaman da uwargidar gwamnan, Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Garba ya bayyana a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, 2021, mutanen gari sun cusa magana ne a bakin Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje.

Goggo
Hafsah Ganduje da Mai gidanta Hoto: www.kanostate.gov.ng
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust da ta dauko wannan labari, ba ta nuna kwamishinan labaran ya yi fashin-baki a kan maganganun da mai dakin gwamnan jihar ta yi ba.

Kalaman matar gwamnan suna ta jawo surutai, har irinsu tsohon kwamishinan ayyuka, Muaz Magaji suna ganin hakan zai iya jawo matsala a tafiyar APC.

A daidai wannan lokaci ne aka ji gwamnan Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya nuna ba ya goyon bayan wani ‘dan takara a zaben jihar da za ayi a 2023.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Sake Kashe Mutum 7 a Jos Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai

Amma masana harkar siyasa suna ganin dabara ce kurum ta ‘yan siyasa gwamna Aminu Masari ya ke yi.

Abin da Matar Gwamna ta fada

Kwanaki ne Farfesa Hafsat Ganduje ta halarci wani taro domin tallafa wa marasa karfi, inda ta nuna irinsu Murtala Sule Garo ne za su hau kan mulki.

Matar gwamnan da aka fi kira da Goggo ta yabi irin kokarin da Garo yake yi a Gwamnatin Mai gidan na ta, ta nua ya cika sharudan zama gwamna a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel