Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Kudancin Kaduna, Mutum Daya Ya Mutu

Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Kudancin Kaduna, Mutum Daya Ya Mutu

  • Wasu yan bindiga sun sake kai hari yankin karamar hukumar Zangon Kataf, dake kudancin Kaduna
  • Maharan sun hallaka wani karamin yaro tare da jikkata mutum ɗaya, sannan suka kona motoci 4
  • Shugaban kwamitin tsaron yankin, John Bala Gora, yace lamarin abun takaici ne matuka

Kaduna - Wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Atuka, wanda aka fi sani da Kangwaza kusa da Jankasa karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna ya yi sanadiyyar mutuwar karamin yaro.

Harin wanda aka kai ranar Litinin da yamma ya bar mutum ɗaya cikin rauni, yayin da aka kona gida ɗaya da motoci huɗu, kamar yadda jaridar Linda Ikeji ta ruwaito.

Da yake bayani ga dailytrust kan lamarin, shugaban kwamitin tsaro na yankin Aytap, Mr. John Bala Gora, yace har yanzun ba'a gane suwa ye suka kai harin ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina: Ku ma ku sayi bindiga ku kare kanku daga 'yan bindiga

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kudancin Kaduna
Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Kudancin Kaduna, Mutum Daya Ya Mutu Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ya kamata jami'an tsaro su kara kokari

Da yake bayyana lamarin a matsayin babban abin takaici, Gora, wanda shine Danmadamin Aytap, yayi kira ga jami'an tsaro su kara zage dantse fiye da baya.

Gora ya kara da cewa akwai bukatar jami'an tsaro su kara kokari fiye da baya wajen dakile kalubalen tsaron dake kara baibaye yankin.

Gora yace:

"Bamu jin dadin irin haka tana faruwa, muna kira ga jami'an tsaro su kara zage dantse wajen kokarin su na shawo kan kalubalen tsaron da ya mamaye yankin mu."

Shin jami'an tsaro sun samu rahoton kai harin?

Da aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna, Muhammed Jalige, ta wayar salula, bai amsa kiran ba bare ya yi tsokaci kan harin.

A wani labarin kuma kungiyar HURIWA ta bukaci Sheikh Pantami ya fito ya yi Allah wadai da kwace ikon da Taliban tayi a Afghanistan

Kara karanta wannan

Babu Wasu Yan Bindiga da Ba'a San Su Ba, Gwamna Ya Zargi Wasu Mutane a Jiharsa

Ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam, HURIWA, ta yi kia ga ministan sadarwa, Isa Pantami, yayi tir da Taliban a Afghanistan.

Kungiyar tace ya kamata ministan ya yi amfani da wannan damar wajen tabbatar da baya kan fatawarsa ta baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262