Nasara daga Allah: Sojoji sun cafke hadimin gwamna dake daukar nauyin 'Unknown Gunmen' a Kudu

Nasara daga Allah: Sojoji sun cafke hadimin gwamna dake daukar nauyin 'Unknown Gunmen' a Kudu

  • Rundunar soji ta bankado wanda yake da hannu dumu-dumu a daukar dawainiyar 'yan bindiga a yankin kudancin Najeriya
  • An gano wani hadimin gwamna, Tochukwu Okeke alias Owo a matsayin mai daukar nauyin 'Unknown Gunmen' a kudanci
  • Okeke yana da kungiya wadanda suke amfani da makaman kare dangi wurin kai wa ‘yan sanda, sojoji da fararen hula farmaki

Kudancin Najeriya - Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar damko hadimin gwamna ne wanda yake kulle-kullen rura wutar ta’addanci a kudu maso gabas.

An bankado wanda ake zargin yana da hannu akan kaiwa mutanen gari da jami’an tsaro farmaki a kudu maso gabacin Najeriya.

Nasara daga Allah: Sojoji sun cafke hadimin gwamna dake daukar nauyin kashe-kashe a Kudu
Nasara daga Allah: Sojoji sun cafke hadimin gwamna dake daukar nauyin kashe-kashe a Kudu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Hadimin gwamna ke daukar nauyin 'Unkwown Gunmen'

PRNigeria ta tattaro bayanai akan yadda wani Tochukwu Okeke alias Owo, hadimin gwamna a kudu maso gabas ya daurewa ‘yan bindiga gindi kamar yadda rundunar division 82 na sojin Najeriya a Enugu suka bankado.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Majiyar ta soji ta bayyana hakan ne inda ta bukaci a boye ta, tace hadimin yana da kungiya mai makaman kare dangi kuma suna kai hari ga ‘yan sanda, sojoji da fararen hula.

Kafin a kama wasu daga cikin shugabannin su a kuma lalata sansaninsu cikin ‘yan kwanakin nan, sun kaiwa ‘yan sanda da sojoji farmaki a Enugu ciki har da ofishin ‘yan sanda na Adani, wata matsayar sojoji dake kan titin Adani-Omoh, ofishin ‘yan sanda na Ezeagu, sansanin sojoji dake titin Orji River-Udi da wata dake kan titin Enugu Abakaliki.

Kungiyar ‘yan ta’addan wacce aka fi sani da “mugaye marasa imani” suna satar makamai a wurin jami’an tsaron da suke kaiwa farmaki.

Majiyar ta sanar da PRNigeria cewa an ragargaji daya daga cikin sansanayensu dake Akpawfu-Amangwunze dake karamar hukumar Nkanu ta yamma inda aka kwato makamai da dama da ababen hawa.

Kara karanta wannan

Muna tarairayar 'yan ta'adda: 'Yan Najeriya sun yi martani kan sha tara da arziki da ke baiwa tubabbu

An gano hakan ne bayan sojoji sun kama shugabansu a Enugu har lokacin da ake rubuta rahoto.

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

Wasu wadanda suka tsallake harin da aka kaiwa matafiya Musulmi a ranar Asabar wurin Gada-Biyu zuwa titin Rukuba dake karamar hukumar Jos ta arewa a jihar Filato, sun bada labarin yadda jami'an tsaro da wasu mutanen kirki suka cece su daga hannun miyagu.

Labarinsu ya bayyana ne bayan da aka gano cewa an sheka mutum 27 a farmakin wanda ya janyo cece-kuce a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito yadda aka kaiwa fasinjoji 90 dake tafiya a motoci biyar farmaki, maharan da 'yan sanda suka kwatanta da matasan Irigwe da masu goyon bayansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng