Sunayen Matafiya fiye da 20 da aka yi wa kisan gilla a Jos, wani ya rasa 'yanuwansa 7
- Wasu miyagu sun tare matafiya a garin Jos, sun hallaka sama da mutum 20
- Kawo yanzu akwai mutane 34 da babu labarin inda suka shiga bayan harin
- An samu jerin sunayen wasu daga cikin matafiyan da aka yi wa kisan gillar
Jos - Jaridar HumAngle ta lalubo sunayen matafiya 26 da aka kashe a hanyar Rukubu, a karamar hukumar Jos ta Arewa, jihar Filato da ke Najeriya.
An kashe matafiya babu gaira-babu dalili
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, an kashe wadannan Bayin Allh ne a hanyar dawowarsu daga taron ibada a gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Matafiyan sun ziyarci garin Bauchi ne domin yi wa al’umma addu’o’i na musamman yayin da aka shiga sabuwar shekarar hijira ta addinin musulunci.
HumAngle ta ce wadanda suka riga mu gidan gaskiyar, suna kan hanyar zuwa Ikare ne, a jihar Ondo.
Wani wanda ya yi rai daga harin, yace suna cikin wata mota mai cin mutane 18 da wata mai cin mutane 22 a lokacin da aka auka masu a ranar Asabar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wadannan miyagun mutane sun tare tawagar motocin da su ka biyo ta hanyar Rukuba, suka kashe mutane har 26, sannan suka ji wa akalla 20 rauni.
Har ila yau an nemi mutane 34 bayan harin, an rasa, an kuma ceto wasu mutum 14 daga cikin matafiyan.
"An kashe mani 'yanuwa 3, 4 sun bace"
Wani mutumi mai suna Alhaji Baido ya rasa ‘yanuwansa uku a wannan mummunan hari; Sule Alhaji Baido, Gambo Alhaji Baido, da Maude Alhaji Baido.
Alhaji Baido yace har yanzu akwai ‘yanuwansa uku da ba a san inda suka shiga ba domin su bakwai ne aka tare, aka kashe uku daga cikin ‘yan gidansu.
Karin Bayani: Jami'an Yan Sanda Na Musamman Sun Ceto Karin Mutum 33 Daga Cikin Musulman da Aka Kaiwa Hari a Jos
Ga sunayen wadanda aka hallaka:
1. Sule Alhaji Baido
2. Mallam Ahmadu
3. Siddi Abubakar
4. Abdulkarim Mumini
5. Mallam Suleiman
6. Mallam Salihu Halilu
7. Mallam Muhammadu
8. Mallam Bello Ori
9. Mallam Abdulkarim
10. Hadimin Mallam Musa Shehu
11. Alhaji Muhammadu Lawal
12. Alhaji Rugga
13. Baa Alhaji Bayo
14. Gambo Alhaji Baido
15. Alhaji Usman Lolo Shagari
16. Mallam Maude Alhaji Baido
17. Ibrahim Haruna
18. Mallam Muhammad II
19. Salihu Hunter
20. Yakubu Mallam Bello
21. Mallam Isyaku
Akwai ragowar mutane hudu da suke cikin wadanda aka kashe, amma jaridar ba ta tantance sunayensu ba.
A baya kun samu labari cewa an yi jana'izar matasan da suka halarci taron zikirin kasa a Bauchi 25 da 'yan bindigan kabilar Irigwe suka hallaka a Gada-biyu.
Rahoton ya tabbatar cewa an bizne wadannan mamatan ne a makabartar Dadinkowa da ke jihar Filato.
Asali: Legit.ng