Da Dumi-Duminsa: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kaduna

Da Dumi-Duminsa: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kaduna

  • Wasu yan bindiga sun sake kai sabon hari a ƙaramar hukumar Zangon Kataf dake kudancin Kaduna
  • Maharan sun kashe aƙalla mutum uku tare da jikkata wata mata, sannan suka kona mota guda ɗaya
  • Hakimin Gora, Mr. Elias Gora, shine ya bayyana haka, yace lamarin ya faru da daren ranar Lahadi

Kaduna - Aƙalla mutum uku suka rasa ransu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Gora Gida, karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Da yake magana da dailytrust, Hakimin Gora, Mr Elias Gora, yace yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi.

Ya kara da cewa wata mata ta samu raunin harbin bindiga sannan kuma maharan sun kona mota guda ɗaya.

Mr. Gora ya kara da cewa mutum biyu daga cikin waɗanda aka kashe sun kasance mahaifi ne da ɗansa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wa ma'aikatan da ke gina matatar man fetur wuta

Yan bindiga sun kai sabon hari kudancin Kaduna
Da Dumi-Duminsa: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakimin yace:

"Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi, inda suka kashe mahaifi da ɗansa da kuma wani mutum ɗaya."
"Yan bindiga sun harbi wata mata ɗaya sannan kuma sun kona mota guda ɗaya a yayin harin."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya ƙi daga kiran wayar da ake masa don jin ta bakinsa.

Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton hukumar yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa game da harin ba a hukumance ba.

A wani labarin kuma Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Yi Magana Kan Kashe Musulmai a Jos

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan matafiya a Jos da sauran kashe-kashen da ake a sassan Najeriya, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Malamai da Dalibin Kwalejin Zamfara Sun tsero Daga Hannun Yan bindiga

Aƙalla mutum 23 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 23 suka jikkata a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta arewa ranar Asabar da safe.

Atiku ya roki yan Najeriya da su baiwa jami'an tsaro haɗin kai domin su fuskanci wannan yaƙin kuma su samu nasara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel