Bayan Nuna Sha'awar Tsayawa Takara a 2023, Attahiru Jega Ya Yi Magana Kan Tsarin Mulkin Karba-Karba

Bayan Nuna Sha'awar Tsayawa Takara a 2023, Attahiru Jega Ya Yi Magana Kan Tsarin Mulkin Karba-Karba

  • Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, yace kai shugabancin kasa wani yanki ba zai haifar da ɗa mai ido ba
  • Jega yace abinda ya fi muhimmanci shine yan Najeriya su zaɓo shugaban da ya dace da halin da ake ciki
  • A cewarsa ko daga wane yanki ya fito indai yana da kwarewar da ake bukata to yan Najeriya su zabe shi

Abuja - Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa tsarin mulkin karɓa-karba ba zai fitar da ƙasar nan daga kalubalen da ta tsinci kanta a ciki ba.

Jega yace wuka da nama na hannun yan Najeriya su zabi nagartaccen mutum wanda zai iya jagorancin kasar nan a 2023, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Farfesa Jega ya yi wannan tsokaci ne yayin wata tattaunawa a cikin shirin kafar watsa labarai ta Arise TV ranar Litinin.

Tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega
Bayan Nuna Sha'awar Tsayawa Takara a 2023, Attahiru Jega Ya Yi Magana Kan Tsarin Mulkin Karba-Karba Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Waye ya dace da mulkin Najeriya?

Tsohon shugaban hukumar INEC, Jega yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A halin da Najeriya ke ciki, muna bukatar nagartaccen mutum wanda yake da kwarewar zama shugaban ƙasa kuma ya fitar da ƙasar nan daga kalubalen da take ciki a yanzu."
"Ko ya fito daga arewa, kudu, gabas ko yamma abinda yafi muhimmanci shine idan jam'iyyun siyasa suka tsaida ɗan takara daga kowane yanki ya fito, hukunci na hannun yan Najeriya."
"Abinda ya kamata yan Najeriya su sani shine ya zama wajibi su natsu su tace sannan su zaɓi wanda ya dace da mulkin kasar nan."
"Wannan maganar da ake ta tsarin mulkin karba-karba ba zai hitad damu daga ƙaƙani kayin da muke ciki a yanzun ba."

Shin ya kamata yan Najeriya su duba shekaru?

A ranar 6 ga watan Agusta, tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya sanya shekarun da yake ganin ya kamata shugaban gaba kada ya wuce su.

IBB yace yana hangen kyakkyawan shugabanci ga mutanen da ba su wuce shekara 60 a duniya ba.

Amma Jega yace sam ba ya goyon bayan maganar tsohon shugaban, inda ya ƙara da cewa shekaru ba abin dubawa bane wajen tantance shugaban kasa na gaba.

A wani.labarin kuma Babu Wasu Yan Bindiga da Ba'a San Su Ba, Gwamna Ya Zargi Wasu Mutane a Jiharsa

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya zargi wasu mutane a yankin kudu maso gabas da rura wutar rikici a yankin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan ya yi wannan zargi ne yayin da yake martani kan dokar zaman gida da yan awaren IPOB suka saka a yankin.

Haramtacciyar kungiyar ta bayyana kulle yankin a kowane mako domin nuna fushinta da kame shugabansu, Nnamdi Kanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel