Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Yi Magana Kan Kashe Musulmai a Jos

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Yi Magana Kan Kashe Musulmai a Jos

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan da akai wa musulmai a Jos
  • Atiku ya kuma roki yan Najeriya da su bada gudummuwarsu wajen taimakawa jami'an tsaro su samu nasara
  • Ya yi jimami da kuma ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayuwarsu tare da fatan samun rahamar Allah

Adamawa - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan matafiya a Jos da sauran kashe-kashen da ake a sassan Najeriya, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Aƙalla mutum 23 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 23 suka jikkata a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta arewa ranar Asabar da safe.

Atiku ya roki yan Najeriya da su baiwa jami'an tsaro haɗin kai domin su fuskanci wannan yaƙin kuma su samu nasara.

Kara karanta wannan

Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Yi Magana Kan Kashe Musulmai a Jos Hoto: dw.com
Asali: UGC

Gwamnati ta kara zage dantse

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kara zage dantse da jajircewa domin dawo da zaman lafiya a faɗin kasar nan.

A jawabin da kakakinsa, Paul Ibe, ya fitar, Alhaji Atiku yace:

"A yanayin halin da kasar mu ta shiga na rashin tsaro, jami'an tsaro na iyakar bakin kokarinsu."
"Amma idan irin waɗannan abubuwan suna faruwa da kuma raɗaɗin dake biyo bayansa zai sa muji kamar ba ayi komai ba."

Atiku ya mika ta'aziyyarsa ga wadanda lamarin ya shafa

Tsohon mataimakin shugaban ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe tare da nuna damuwarsa kan yadda suka haɗu da ajalinsu cikin mummunar yanayi.

Ya kuma yi Addu'a tare da fatan Allah ya kawo karshen halin da Najeriya take ciki kuma ya gafartawa mutanen da aka kashe.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Jos: Sako mai ratsa zuciya da Ahmed Musa ya aikewa gwamnati

A wani labarin kuma wasu daga cikin Malamai da Dalibin Kwalejin Zamfara Sun tsero Daga Hannun Yan bindiga

Malamai biyu da ɗalibi ɗaya daga cikin waɗanda aka sace a kwalejin noma dake Bakura, jihar Zamfara sun tsero daga hannun yan bindiga, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kwalejin, Ali Atiku , shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin.

Yace hukumar makaranta ta gano cewa maharan sun yi awon gaba da ɗalibai 15 da kuma malamai guda uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262