Hotunan motocin alfarma na dan kwallo Emmanuel Adebayor, sun kai darajar N300m

Hotunan motocin alfarma na dan kwallo Emmanuel Adebayor, sun kai darajar N300m

  • Emmanuel Adebayor, fitaccen dan kwallon kafa, matashi ne mai matukar son more rayuwa da hawa kasaitattun motoci tsadaddu
  • Tsohon dan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal din ya bayyana hotunan motocinsa kirar Rolls-Royce da Mercedes Benz G65 wanda zasu kai miliyan 200
  • Tsadaddar Rolls-Royce din ta ja hankalin mutane da dama sakamakon yadda ya sanya lambar motar ya zama na musamman 004 SEA

Togo - Emmanuel Adebayor yana matukar son more rayuwa da hawa motoci masu tsadar gaske tun daga mota kirar Rolls Royce, Mercedes Benz G65 tana daya daga cikin tsadaddun motoci wadanda tsohon dan kungiyar Arsenal din ya mallaka.

Motar Rolls-Royce mai matukar tsada ta kere duk wasu motocin da ya mallaka, kuma ya sanya mata lambar mota ta musamman 004 SEA.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

Hotunan motocin alfama na dan kwallo Emmanuel Adebayor, sun kai darajar N300m
Hotunan motocin alfama na dan kwallo Emmanuel Adebayor, sun kai darajar N300m. Hoto daga @e_adebayor
Asali: Instagram

Motar tasa ta kai £360,000 wanda ya kai N200,000,000.

Sannan a cikin garejinsa akwai wata Mercedes Benz G65 wacce takai kimar £170,000 wanda yakai N95,000,000, hakan ya gigita mutane da dama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

SunSports sun ruwaito yadda Rolls-Royce Phantom din ta ja hankalin mutane da dama.

Adebayor ya bayyana hotunan motocinsa a shafinsa na Instagram don ya nunawa mabiyansa.

Ya taba bayyana dalilinsa na kin bayar da ko sisinsa wurin yaki da cutar Coronavirus a Togo.

Ya bayyana hotunan kasaitattun motocinsa, motarsa kirar Rolls-Royce mai kalar goro wacce ta dace da inda aka ajiye ta kuma tsadarta ta kai naira miliyan 200- wanda hakan yake nufin sunayensa na ainihi, Sheyi Emmanuel Adebayor.

Matashin mai shekaru 37, ya wallafa hotonsa da motar wacce yayi tsokaci da “Ina son tsarin rayuwata.”

Adebayor, wanda yayi wa kungiyar Paraguayan Olimpia wasa, ya wallafa hotunan jerin motocinsa wadanda ya adana a wani wuri mai burgewa a cikin katafaren gidansa dake Accra, kasar Ghana a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga gina shaguna a kan titunan Kantin Kwari

Wata babbar kotu a Kano da ta samu shugabancin Mai shari'a S. B Namallam ta dakatar da gwamnatin jihar Kano daga gina shaguna a kan titunan kasuwar Kantin Kwari.

A cikin kwanakin nan ne gwamnatin jihar Kano ta bada fulotai a tsakiyar layikan Ta'ambu da Bayajidda dake kasuwar Kantin Kwari, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan al'amari babu shakka ya janyo cece-kuce tare da suka wanda jama'a suka dinga damuwa kan batun tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel