Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga gina shaguna a kan titunan Kantin Kwari

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga gina shaguna a kan titunan Kantin Kwari

  • Babbar kotu dake zama a jihar Kano ta dakatar da gwamnatin Kano daga gina shaguna a kan titunan kasuwar Kwari
  • Kamar yadda mai shari'a S. B Namallam ya yanke a kotun, yace a dakata da gina shagunan har sai an kammala jin korafin
  • Tun farko gwamnatin Kano ta bada fulotai domin gina shaguna tsakanin layin Ta'ambu da Bayajidda dake kasuwar Kwari

Kano - Wata babbar kotu a Kano da ta samu shugabancin Mai shari'a S. B Namallam ta dakatar da gwamnatin jihar Kano daga gina shaguna a kan titunan kasuwar Kantin Kwari.

A cikin kwanakin nan ne gwamnatin jihar Kano ta bada fulotai a tsakiyar layikan Ta'ambu da Bayajidda dake kasuwar Kantin Kwari, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Amurka ta bukaci gaggauta garkame Abba Kyari cikin Kurkuku kafin ya gurfana a kotu

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga gina shaguna a kan titunan Kantin Kwari
Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga gina shaguna a kan titunan Kantin Kwari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Wannan al'amari babu shakka ya janyo cece-kuce tare da suka wanda jama'a suka dinga damuwa kan batun tsaro.

Su waye suka kai kara gaban kotu?

Wata kungiyar 'yan kasuwa masu kishi da suka hada da: Shehu Bukar Makoda, Yushau Alaskan, Auwalu Buhari, Kabiru Isma'il, Salihu Baita da kuma gamayyar kungiyar kanana da matsakaitan 'yan kasuwan Kano suka maka kamfanin RAZ, hukumar tsara birane da habaka ta jihar Kano tare da hukumar kula da filaye na jihar Kano a gaban kotu kan wannan cigaban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanne hukunci alkali ya yanke?

Bayan sauraron lauyan masu kara, Abba Hikima, wanda ya gabatar da kokensu, kotun ta dakatar da wannan cigaban kan tituna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kotu ta bada umarnin wucin-gadi na dakatar da wanda ake kara na farko ko jami'anta da cigaba da gina shaguna a kan titunan Ta'ambu da Bayajidda a kasuwar Kantin Kwari dake Kano har dai an kammala shari'ar.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Umarnin ya haramtawa mai kare Kansa na farko daga shi ko wata kungiya daga bari a yi shagunan da zasu kare masu kara tare da take musu hakkinsu na walwala ta hanyar saka shaguna kan layikan Ta'ambu da Bayajidda na kasuwar Kantin Kwari dake Kano har sai an gama shari'a.
Ana umartar kowa da ya tsaya a matsayarsa har sai an kammala sauraro tare da hukunci kan wannan kara wacce za a yi shari'ar a ranar 19 ga watan Augustan 2021, umarnin yace.

Sojoji sun cafke mutum 8 da ake zargi da hannu a bindige mata 3 a Bassa, Filato

Rundunar Operation Safe Heaven a ranar Talata, 10 ga watan Augustan 2021 ta kama mutane 8 da ake zargin suna da hannu a harbin wasu mata 3 a wata gona dake kusa da Rafin Bauna dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Rundunar ta amsa kiran gaggawar da aka yi mata akan kisan mata 3 da suke kusa da Rafin Bauna wadanda wasu ‘yan bindiga suka harbe, PR Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: DSS Ta Bi Umarnin Kotu, Ta Gabatar da Dukkan Hadiman Sunday Igboho a Kotu

Take anan rundunar tayi gaggawar isa wurin inda ta riski mata 3 cikinsu har 2 sun mutu daya kuma rai a hannun Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: