Nasara: Bidiyon 'yan ISWAP-Boko Haram na tururuwar tuba a Mafa dake Borno
- Sama da 'yan ta'addan ISWAP-Boko Haram 1,500 ne suka mika wuya ga hukumomin tsaro a Borno
- Kamar yadda bidiyo ya nuna, an ga jerin 'yan Boko Haram, matansu da 'ya'yansu suna fitowa daga daji cikin layi
- Ana tsammanin sama da 'yan Boko Haram 2000 zasu mika wuya ga sojoji a yankin tafkin Chadi a cikin wannan makon
Borno - A halin yanzu, dakarun sojin Najeriya sun karba kwamandoji da mambobin Boko Haram da suka tuba sama da 1,500 a gagarumar tururuwar da tsoffin 'yan ta'addan ke yi wurin tuba.
A wani bidiyo da PRNigeria ta samu, an ga tubabbun 'yan ta'adda masu tarin yawa, iyalansu da suka hada da mata tare da kananan yara, suna fitowa a dogon layi daga dajikan yankin.
Wadanda ke fitowa daga dajikan sun gangara gaban sojoji dake Mafa, daga baya aka gano.
Wasu daga cikin manyan kwamandojin kungiyar, da suka hada da Adamu Rugurugu da iyalansa sun mika wuya ga sojojin a wurare daban-daban dake jihar Borno.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasu daga cikin 'yan ta'addan sun mika wuya tare da iyalansu a Bama, Mafa da Gwoza a cikin ranakun karshen mako.
PRNigeria ta gano cewa rundunar sojin ta dinga gangami tare da wayar da kai a kabilar Kanuri da Hausa a cikin kwanakin nan, hakan yasa da yawan 'yan ta'addan sun bar ta'addanci tare da mika makamansu.
Me yasa 'yan ta'addan suke mika wuya?
Wata babbar majiyar sirri daga cikin rundunar ta sanar da PRNigeria cewa 'yan ta'ddan na barin sansaninsu ne suna mika wuya ga hukumomi sakamakon wa'azi da wayar da kai da malamai ke yi musu.
Ya ce kusan 'yan ta'adda 2000 ne ake tsammanin zasu mika wuya ga hukumomi a yankin tafkin Chadi saboda wayar da kai tare da ayyukan sojojin Najeriya.
Mummunar Gobara ta yi wa Gidan Talabijin Kurmus a Jihar Ogun
Wata kazamar gobara ta kone gidan talabijin din Hi-Impact, gidan watsa shirye-shiryen talabijin na HD na farko a Najeriya dake jihar Ogun.
Bangaren watsa shirye-shiryen yana harabar Hi-Impact Planet Amusements Park & Resort dake wurin kilomita 12 a titin Lagos zuwa Ibadan a Ibafo dake karamar hukumar Obafemi Owode jihar Ogun.
Daily Trust ta ruwaito cewa, gobarar ta fara ne tun ranar Alhamis kuma bangaren watsa shirye-shiryen ya cinye kone kurmus.
Asali: Legit.ng