Gada ta ruguje a Jigawa, ta hallaka matafiya ciki har da masu neman aikin soja

Gada ta ruguje a Jigawa, ta hallaka matafiya ciki har da masu neman aikin soja

  • Wata gada ta ruguje a wani yankin jihar Jigawa kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, a cikin wadanda suka mutu har da wasu masu neman aikin soja da basu samu ba

Jigawa - Akalla mutane 21, ciki har da mutane 11 masu neman aikin soja, an ba da rahoton mutuwarsu a ranar Lahadi yayin da wata gada ta ruguje a Karamar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa.

Mazauna garin sun ce gadar ta rushe ne sakamakon ambaliyar ruwa.

Shugaban kungiyar fararen hula ta jihar Jigawa, Musbahu Basirka, ya shaida wa Premium Times cewa wadanda abin ya rutsa da su na cikin motar bas ne daga Kano zuwa Adamawa lokacin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Yanzu-Yanzu: Gada ta ruguje a Jigawa, ta hallaka matafiya da dama
Taswirar jihar Jigawa | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mista Basirka ya ce wadanda suka mutu sun hada da wata matashiya amma an bayar da rahoton cewa daya daga cikin masu neman aikin sojan ya tsira da karayar kafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani Sanata ya makale a hanyar Abuja saboda ambaliyar ruwan sama

Wasu sassan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja zuwa Okene sun kasance cikin ambaliya a ranar Asabar 7 ga watan Agusta wacce ta mamaye su bayan ruwan sama na awa hudu.

Daya daga cikin yankunan da abin ya shafa shi ne tsakanin Kwali da Abaji. Ambaliyar ta sa matafiya sun makale yayin da motoci daga Abuja ba za su iya wucewa zuwa Lokoja, Okene da sassan kudanci ba.

Kimanin motocin bas guda uku ne rahotanni suka ce ambaliyar ta kwashe su.

Daga cikin daruruwan matafiya da suka makale har da Sanata daga gundumar Kogi ta yamma, Sanata Smart Adeyemi, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Yadda jami'in tsaro ya harbi wata yarinya a garin warwason abinci a wurin biki

Wata budurwa ta bakunci lahira yayin da take lalata da saurayinta a mota

A wani labarin, Mutuwa ta dauke wata budurwa mai suna Gabrielly Dickson a yayin da suke tsaka da fasikanci da saurayinta mai shekaru 26 a cikin mota.

An garzaya da budurwar mai shekara 15 zuwa asibiti ne bayan saurayin nata da yake fasikanci da ita ya lura cewa ta fita daga hayyacinta, in ji Aminiya.

’Yan sanda da ke binciken lamarin sun ce saurayin, wanda ake kira “babban mai taimako”, ya shaida musu cewa yana cikin saduwa da ita a cikin mota ne ya lura labbanta da fatar jikinta sun koma fari fat, hannuwanta kuma sun jujjuye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel