Buhari ga turawan yamma: Ba ma bukatar sojojinku, hannun jari muke bukata

Buhari ga turawan yamma: Ba ma bukatar sojojinku, hannun jari muke bukata

  • Shugaba Buhari ya bayyana gaskiyar abubuwan da Afrika ke bukata daga turawan yammaci
  • A cewar Buhari, Afrika ba ta bukatar sojojin yaki, don haka a daina turo sojoji a dukufa wajen gina nahiyar
  • Ya kuma bayyana cewa, dakarun da Afrika ke dashi sun isa duk wani yaki da zai iya tashi a yankin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kasashen Afrika basa bukatar dandazon sojojin Amurka da sauran dakarun turai don magance matsalolin da suke fuskanta na ta'addanci.

A cewar shugaban, kasashen Afrika na da dakarun da za su iya tunkarar kowane irin yaki ne ba tare da hannun Amurka da wata kasar turai ba, duk da cewa ya amince da kasashen Afrika na bukatar wadatattun kayan aiki.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi martani yayin da matar marigayin kanal ta yi ikirarin cewa kashe mijinta aka yi

Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata makala da ya wallafa a jaridar Financial Times jiya Lahadi 15 ga watan Agusta.

Buhari ga Turawa: Ba ma bukatar sojojinku, hannun jari muke bukata
Shugaba Muhammadu Buhari | Hoto: fmic.gov.ng
Asali: UGC

Legit Hausa ta tattaro cewa, shugaban ya kuma yi nuni da cewa, tallafin Amurka da sauran kasashen Turai ba zai taba kawar da ta'addanci ba, inda ya buga misali da cewa, ga kasar Afghanistan ta zama yadda ta zama bayan janyewar dakarun Amurka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Buhari kan ficewar sojojin hadaka na kasashen duniya karkashin jagorancin Amurka daga Afghanistan bayan shekaru 20, kwanaki 10 kadai ya basu damar karbe kasar, yana mai jaddada cewa:

"Karfin soja zai iya rage wa ta'addanci karfi amma zai iya dawowa bayan kawar da shi".

Ba ma bukatar sojojin yaki

Hakazalika, shugaba Buhari ya sake jaddadawa a cikin makalar cewa:

"Bai kamata a tsammaci cewa Amurka da kawayenta na kasashen Turai za su dauki tsaron sauran kasashe da muhimmnanci ba kuma har abada. Afirka na da isassun dakaru na kanta.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya za su yi wa tubabbun 'yan ta'adda karatun gyaran hali

"Sai dai za a iya taimakawa da kayan aiki da bayanan sirri da tsare-tsare."

Meye Afrika ke bukata?

Da yake bayyana bukatar da nahiyar Afrika ta fi bukata daga kasashen duniya, shugaba Buhari ya bayyana cewa, a halin yanzu, nahiyar na bukatar cike babban gibin da ke bukatar ciko, wanda a cewarsa, shine zuba manyan hannayen jari.

"Abin da muke bukata daga Amurka shi ne cikakkiyar alakar kasuwanci domin rage girman gibin da ke tsakanin yawan al'umma da kuma karuwar tattalin arziki.
"Abin da muka fi bubata shi ne zuba jari a ayyukan raya kasa. Layukan dogo da sufuri za su samar da damarmaki ga wadanda ba su da su.
"Duk da cewa kasashen Afirka shida daga cikin 10 da tattalin arzikinsu ke saurin habaka, habakar tattalin arzikin nahiyata ba shi da yawan da zai iya magance matsalar yawan al'umma.

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur

Kara karanta wannan

Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta

A wani labarin daban, Rahoton da muke samu daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur.

Legit.ng Hausa ta samo wata sanarwar mai ba shugaba shawari na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, inda ta bayyana rattaba hannun shugaban a yau Litinin 16 ga watan Agusta, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel