Khalifan Tijjaniyya Ya Magantu Kan Kisan da Aka Yiwa Zakirai Fiye da 20 a Jos

Khalifan Tijjaniyya Ya Magantu Kan Kisan da Aka Yiwa Zakirai Fiye da 20 a Jos

  • Khalifan Tijjaniyya a Najeriya, Muhammad Sanusi II, ya nemi gwamnati ta sauke amanar da Allah ya ɗora mata
  • Tsohon Sarkin Kano ya yi kira da a kame duk masu hannu a kisan a hukunta su yadda ya dace
  • Sanusi ya kuma yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe da kuma Sheikh Dahiru Bauchi

Plateau - Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga gwamnatin tarayya, gwamnatin Filato da jami'an tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka kashe matafiya fiye da 20 a Jos.

Tsohon sarkin Kano yace ya zama wajibi gwamnati ta sauke amanar da Allah ya bata na kare rayukan al'umma, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Asabar da ta gabata wasu mutane suka tare motocin matafiyan, waɗanda yan ɗarikar tijjaniyya ne a kan hanyarsu ta komawa gida.

Kara karanta wannan

Wannan ba shine farko ba: Izala ta yi martani kan kashe Musulmai da aka yi a Jos

Khalifan Tijjaniyya a Najeriya, Muhammad Sanusi II
Khalifan Tijjaniyya Ya Magantu Kan Kisan da Aka Yiwa Zakirai Fiye da 20 a Jos Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Matafiyan sun baro Bauchi bayan halartar taron zikiri a gidan babban shehin malamin Tijjaniyya, Sheikh Ɗahiru Bauchi, zasu koma gida jihar Ondo, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A binciko duk masu hannu a hukunta su

A wani jawabi da khalifan Tijjaniyya, Sunusi II, ya fitar, ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnati ta binciko masu hannu kuma a hukunta su.

A jawabinsa yace:

"Gwamnati ta tsaya a kan amanar da Allah Ya ba ta na kare rayuwar al'umma, a yi cikakken bincike a kan waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi a kuma yi musu hukuncin da ya dace."

Muna kira ga yan Tijjaniya su kwantar da hankali

Muhammad Sanusi ya kuma yi kira ga yan ɗarikar Tijjaniyya da su kwantar da hankulansu kada su ɗauki doka a hannunsu.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Khalifa yace:

"A bai wa jami'an tsaro damar yin aiki yadda ya dace. Muna roƙon Allah ya bayyana waɗanda suka yi wannan ta'addancin kuma ya ba da ikon yin adalci."

Daga karshe, Khalifa Sanusi ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma Sheikh Dahiru Bauchi.

A wani labarin kuma Wata Sabuwa, Shugaba Buhari Ya Killace Kansa Bayan Dawowa Daga Landan

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , tare da jami'an gwamnati da suka raka shi sun killace kansu bayan shafe sama da makwanni biyu a Landan.

Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shine ya tabbatar da haka ga Channels tv ranar Lahadi.

Shehu ya bayyana cewa shugaban ya ɗauki wannan matakin ne domin biyayya ga dokokin hukumar dakile yaɗuwar cututtuka (NCDC).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel