Dan majalisar wakilai mai ci a jam'iyyar PDP ya rigamu gidan gaskiya
- Dan majalisa daga jihar Ondo ya riga mu gidan gaskiya bayan karamar jinya da yayi a asibiti
- Hon Omolafe Adedayo Isaac ta kasance dan majalisa mai wakilatar Akure ta Arewa da Kudu
- Hakazalika ya rike mukamai da dama, hakazalika babban jigo ne a jam'iyyar adawa ta PDP
Dan majalisar da ke wakiltar Akure ta Arewa da Akure ta Kudu a majalisar wakilai, Hon Omolafe Adedayo Isaac aka “Expensive”, ya rasu.
Hon Omolafe ya rasu da misalin karfe 2 na safe a wani asibiti mai zaman kansa a Akure, babban birnin jihar Ondo.
An zabi Omolafe a Majalisar Dokoki ta kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, The Nation ta ruwaito.
An zabe shi shugaban wata karamar hukuma kuma yayi aiki a matsayin Kodineta na shirin SURE-P a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Shugabancin 2023: A karshe Wike ya magantu kan Atiku, yace bai san kudirin tsohon mataimakin shugaban kasar ba
Kakakin Jam’iyyar PDP na Ondo, Kennedy Peretei, wanda ya tabbatar da mutuwar, ya bayyana shi a matsayin dan siyasar talaka wanda za a yi kewar sa.
Peretei ya ce mutuwarsa babbar illa ce ga jam'iyyar.
Matar tsohon shugaban kasa, Hadiza Shagari ta mutu bayan fama da cutar korona
A wani bangare guda, Allah ya yi wa Hadiza Shagari, matar marigayi tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari rasuwa, tana da shekaru 80 a duniya, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Wata sanarwa da ‘dan tsohon shugaban kasar, Bala Shagari ya fitar, ya bayyana cewa ta mutu ne sakamakon cutar korona a cibiyar killace masu cutar da ke Gwagwalada.
Ya kuma bayyana cewa za a yi jana’izarta a yau Alhamis, 12 ga watan Agusta, bayan sallar la’asar a babban masallacin kasa da ke Abuja, Solacebase ta ruwaito.
Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur
A wani labarin, Rahoton da muke samu daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur.
Legit.ng Hausa ta samo wata sanarwar mai ba shugaba shawari na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, inda ta bayyana rattaba hannun shugaban a yau Litinin 16 ga watan Agusta, 2021.
Asali: Legit.ng