Tsadar abinci: Ba fa zai yiwu mu yi kasa da farashin buhun shinkafa ba inji ‘Yan kasuwa

Tsadar abinci: Ba fa zai yiwu mu yi kasa da farashin buhun shinkafa ba inji ‘Yan kasuwa

  • Hukumar PCACC a Kano ta na kokarin ganin kudin buhun shinkafa ya sauko kasa
  • ‘Yan kasuwa sun sanar da shi cewa sauyin farashin da aka samu ba daga su ba ne
  • A ‘yan kwanakin nan, kudin buhun shinkafa ya tashi daga N19000, ya kai N23000

Kungitar RIPAN ta masu aikin gyara shinkafa a Najeriya, ta reshen jihar Kano ta yi bayanin abin da ya sabbaba tashin farashin da ake fuskanta a yau.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto inda aka ji wani daga cikin ‘ya ‘yan wannan kungiya ya na karin-haske a kan abin da ya sa buhu ya kai N23, 000.

Alhaji Abba Dantata a madadin kungiyar RIPAN, ya zanta da ‘yan jarida tare da hukumar PCACC ta jihar Kano, bayan wani zama da su ka yi a makon nan.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ba za ta bari a shigo da shinkafa ba

Ba laifin mu ba ne, komai ya kara kudi - RIPAN

A zaman da su ka yi da Muhuyi Magaji-Rimingado a garin Kano, Vanguard ta rahoto Abba Dantata ya na fada wa manema labarai cewa kudin aiki ya karu.

Ya ce:

“Ba zai yiwu mu saida buhun shinkafa mai cin kilogram 50 a kan kasa da N23, 000 ba.”
"Kudin da mu ke kashewa wurin aiki ya tashi. Daga Afrilu zuwa yau, ton din shinkafa mai samfarera ya tashi daga N180, 000, yanzu ya koma N225, 000.”

Abba Dantata yake cewa an samu sauyi yanzu wajen canjin kudin kasar waje da ake amfani da su domin sayen na’urori da gyaran kayan aikin gyaran shinkafar.

Shinkafan gida
Buhunan shinkafan gida Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: RIPAN ta yarda ta karya kudin buhun shinkafa ya kai N19, 000

"Haka zalika tashin da kudin bakin mai ya yi, ya taimaka wajen sauyin farashin shinkafa da aka samu."

CBN sun daina ba mu bashi mai saukin ruwa

A cewar ‘dan kasuwar, a 2020 ne bankin CBN ya janye tallafin Agro Fund da ya ke ba manoman shinkafa, an yi wannan ne ba tare da an sanar da su za ayi hakan ba.

“Wasunmu suka tafi bankunan ‘yan kasuwa su ka ci bashi da ruwan 20%, 22%, har zuwa 25%.”

PCACC ta ce ta kira wannan taro ne domin a samu saukin abinci, amma abin da kamar wuya.

Dazu kun ji cewa da mutum kusan miliyan hudu cikin talauci, Zamfara ce gaba a yawan talakawa a jihohin Najeriya, Ekiti ce jiha mai mafi karancin adadin talakawa.

Alkaluma sun ce talakawa 35,267,966 su ke zaune a Najeriya, Zamfara kadai ta tashi da 3,836,484.

Asali: Legit.ng

Online view pixel