DSS sun tsare tsohon gwamna da wasu 'yan APC 5 kan zargin taron sukar Buhari

DSS sun tsare tsohon gwamna da wasu 'yan APC 5 kan zargin taron sukar Buhari

  • Jami’an DSS sun tirke tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow inda ya sha tambayoyi akan wani taro da ya halarta
  • Rahotanni sun tabbatar da yadda Bindow da wasu manyan masu fadi a ji na APC suka halarci wani taro na juyawa Buhari baya
  • An ji wasu maganganu da aka yi ta tattaunawa a taron wanda cikin wadanda suka halarta suke yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari fatan mutuwa

Yola, Adamawa - Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow ya sha tarin tambayoyi akan wani taron juyawa Buhari baya da ya halarta tare da wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC guda 5.

A ranar Laraba, 11 ga watan Augusta ne tsohon gwamnan ya sha tambayoyin a gaban hukumar tamkar tamabayoyin kurar hali.

DSS sun tsare tsohon gwamna da wasu 'yan APC 5 kan zargin taron sukar Buhari
DSS sun tsare tsohon gwamna da wasu 'yan APC 5 kan zargin taron sukar Buhari. Hoto daga GOVT House Yola
Asali: Facebook

Ta yaya tsohon gwamnan ya amsa gayyatar DSS?

TheCable ta ruwaito yadda hadimin gwamnan na harkokin watsa labarai, Sadiq Abdullateef ya bayyana yadda Bindow ya amsa gayyatar DSS inda yace har sun sako shi.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta yi wa tsohon Gwamna da wasu mambobin APC 5 tambayoyi kan taron kin jinin Buhari

Kamar yadda jaridar ta tabbatar, Bindow tare da wasu mutane 5 da suka hada da:

1. Kabiru Mijinyawa, tsohon kakakin majalisar jihar Adamawa

2. Suleiman Adamu, mukaddashin shugaban APC na Yola ta kudu

3. Mustapha Barkindo, tsohon mai baiwa Bindow shawara

4. Abubakar Umar Sirimbai, tsohon kwamishina

5. Yusha’u Adamu, sun yi taron sirri.

Maganganu akan taron sirri sun bayyana inda aka ji wasu fusatattun 'yan jam'iyyar daga cikin wadanda suka halarci taron suna yi wa Buhari fatan mutuwa.

DSS ta gayyacesu bisa maganganun da aka ji akan bayyanar abubuwan da suka tattaunawa a taron.

Muna tarairayar 'yan ta'adda: 'Yan Najeriya sun yi martani kan sha tara da arziki da ke baiwa tubabbu

Cece-kuce sun yawaita a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter bayan bayyanar hotunan sojoji suna baiwa tubabbun kwamandojin mayakan Boko Haram kayan abinci.

Kwamandojin Boko Haram sun zubar da makamansu sannan sun yi mubaya’a ga sojojin Operation Hadin Kai, The Cable ta wallafa.

Kara karanta wannan

SWC ta dakatar da Shugaban APC mai yi wa Buhari fatan ya mutu, Osinbajo ya hau mulki

A wata takarda ta ranar Litinin, Kakakin sojin, Onyema Nwachukwu, ya wallafa hotunan kwamandojin Boko Haram inda yace Musa Adamu, kwararre akan hada bama-bamai cikin ‘yan Boko Haram yana daya daga cikin wadanda suka tuba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel