Wata Sabuwa: Shugaba Buhari Ya Killace Kansa Bayan Dawowa Daga Landan
- Shugaban ƙasa, Buhari, tare da manyan jami'an gwamnati da suka je Landan sun keɓe kansu na tsawon kwana 10
- Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka ranar Lahadi
- Yace shugaban ya ɗauki wannan matakin ne domin kiyaye dokokin hukumar NCDC na waɗanda suka dawo daga waje
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, tare da jami'an gwamnati da suka raka shi sun killace kansu bayan shafe sama da makwanni biyu a Landan.
Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shine ya tabbatar da haka ga Channels tv ranar Lahadi.
Shehu ya bayyana cewa shugaban ya ɗauki wannan matakin ne domin biyayya ga dokokin hukumar dakile yaɗuwar cututtuka (NCDC).
Shehu yace:
"Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari tare da waɗanda suka raka shi zuwa birnin Landan sun killace kansu domin kiyaye dokokin hukumar NCDC ga mutanen da suka yi tafiya zuwa kasashen waje."
An kulle ofishin jakandancin Najeriya a Landan
Tuni aka garkame ofishin jakadancin Najeriya dake Landan bayan samun wasu jami'ai ɗauke da cutar COVID19, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.
Rahoto ya nuna cewa an ɗauki wannan matakin ne domin duk waɗanda suka yi mu'amala da su killace kansu na tsawon kwana 10.
Su waye suka raka Buhari Landan?
Kusoshin gwamnatin tarayya da suka marawa Buhari baya zuwa Landan sun haɗa da, ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba.
Sauran sun haɗa da, Darakta Janar na hukumar Fasaha, Ambasada Ahmad Rufa'i Abubakar, da mai bada shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno.
A ranar 26 ga watan Yuli, Shugaba Buhari, ya tafi Landan na kasar Burtaniya domin halartar taron haɓɓaka ilimi na duniya.
A wajen wannan taron ne, Buhari ya sha alwashin kara kasafin ɓangaren Ilimi da kashi 50.
A wani labarin kuma A wani labarin kuma gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ya bayyana yadda yake shan matsin lamba daga iyalai da abokan arziki kan takarar shugaban ƙasa.
Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin wasu ƙungiyoyi dake neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023.
Muhammed, wanda ya nemi a bashi mako 3 ya yi shawara, ya sake neman a sake ba shi lokaci.
Asali: Legit.ng