Yadda jami'in tsaro ya harbi wata yarinya a garin warwason abinci a wurin biki

Yadda jami'in tsaro ya harbi wata yarinya a garin warwason abinci a wurin biki

  • Bikin aure ya watse yayin da harsashin bindiga ya kubuta ya harbi wata yarinya a wajen aure
  • An ruwaito cewa, wani jami'in tsaro ne ya harba bindigarsa bisa kuskure, lamarin da ya jawo tashin hankali
  • Hukumar tsaron da abin ya shafa bai tabbatar da faruwar lamarin ba, amma majiyoyi sun tabbatar da haka

Akwa Ibom - Bikin aure a Uyo, Jihar Akwa Ibom ya watse a ranar Asabar bayan da harsashin bindiga ya hallaka wata yarinya mai shekaru 15.

Lamarin ya biyo bayan harbi cikin kuskure da wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC da aka kawo don samar da tsaro a wurin taron ya yi.

Wacce aka kashe, Veronica Kufre, tana karbar magani a sashin kulawa mai zurfi na wani asibiti mai zaman kansa a babban birnin jihar bayan asibitoci uku sun ki karbar ta.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a unguwar Nsukara, kusa da babban harabar jami'ar Uyo a lokacin da ake kokawar karbar abin sha da abinci a bikin.

Yadda jami'in tsaro ya harbi wata yarinya a garin warwason abinci a wurin biki
Jami'an tsaron NSCDC | Hoto: guardian.ng
Asali: Twitter

Wata majiyar wajen auren, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Punch cewa, jami’an tsaron, wadanda ake zargin sun harba harsashin, sun je bikin ne domin wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Ta yaya abin ya faru:

Majiyar ta ce matsala ta fara ne lokacin da:

"Jami’an tsaron biyu suka shiga cikin sauran baki don karbar abinci amma abin takaici, bindigarsu na hannunsu sai kwatsam aka ji harbin ba zata lamarin da ya kai ga ma'auratan da sauran bakin tserewa don tsira.
“Amma daya daga cikin su ya yi saurin mayar da hancin bindigar zuwa kasa sannan ya jefa sauran harsasan a ciki. Duk da haka, gutsutsayen sun riga sun bugi wacce aka kuskura da ke kusa da jami’in tsaron.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayin da ‘yan bindiga suka bude wuta kan matafiya a Jos

“Da farko, mun yi tsammanin harbe-harben da aka saba yi ne jami’an tsaro za su rika harbawa yayin jana’iza, daurin aure, da sauran bukukuwa don karawa biki armashi Amma lokacin da yarinyar ta fadi kasa da zubar da jini, mun gano shaidan na aiki don ture farin cikin mu."

Mai magana da yawun hukumar NSCDC a jihar, Ukeme Umanah ya fadawa gidan Talabijin na Channels a hirar wayar tarho cewa bayanai game da lamarin har yanzu suna cikin rudani.

Amma, ya ce kwamandan rundunar na jihar, Abidemi Majekondunmi, ya fara aiki da tsari don tabbatar da abin da ya faru, lura da cewa wacce aka kuskura na cikin tsaka mai wuya.

Ya ba da tabbacin cewa NSCDC za ta fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin da zaran an kammala bincike.

An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

A baya, rundunar tsaro ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH) a jihar Filato, ta cafke wasu mutane 12 da ake zargi da aikata kashe-kashe da safiyar Asabar a kan hanyar Rukuba ta karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar, in ji rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

A sabbin rahotanni da suka shigo a yau kuwa, Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane 20 ne ya zuwa yanzu a cafke da hannu wajen kisan musulmai 25 a wani yankin jihar Filato.

Manjo Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Asabar a garin Jos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.