Ballewar rikici: Jami'ar Jos ta dage jarrabawar zango bisa kashe musulmai da aka yi

Ballewar rikici: Jami'ar Jos ta dage jarrabawar zango bisa kashe musulmai da aka yi

  • Jami'ar Jos ta dage jarrabawar dake gudana yanzu haka a makarantar saboda barkewar rikici
  • Wannan ya biyo bayan kashe wasu matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi jiya Asabar a jihar Filato
  • Hukumar gudanarwar makarantar ta dage jarrabawar har sai an samu sabuwar sanarwar zaman lafiya

Hukumar gudanarwa ta jami’ar Jos ta dakatar da ci gaba da gudanar da jarabawa zangon karatu na na biyu na shekarar 2019/2020 cikin gaggawa bayan barazanar tsaro da ya dunfaro a jihar Filato, The Nation ta ruwaito.

Sanarwar da Mataimakin Magatakarda, Abdullahi Abdullahi, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa:

“Bayan barkewar rashin tsaro da ya faru a wasu sassan garin Jos, wanda ya sa Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Jos, Karamar Hukumar ta Arewaci, hukumar gudanarwar Jami’ar Jos ta amince da dakatar da jarabawar zangon karatu na biyu na 2019/2020.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Yanzu-Yanzu: Jami'ar Jos ta dage jarrabawar zango bisa kashe musulmai da aka yi
Jami'ar Jos | Hoto: nigerianscholars.com
Asali: UGC

“Sakamakon haka, an dakatar da duk jarabawar da aka shirya tsakanin Litinin 16 zuwa Asabar 21 ga Agusta 2021 har sai an samu sabuwar sanarwa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa:

“Ana sanar da dukkan Dalibai na Jami’ar da ke zaune a dakunan kwanan dalibai da su kasance a cikin dakunan kwanan su da kuma gujewa motsin da ba dole ba kamar yadda hukumar gudanarwa ke aiki ba dare ba rana tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da Gwamnatin Jihar Filato don tabbatar da cewa an kare rayuka da dukiyoyin membobin Jama'ar Jami'ar musamman dalibai.
"An kuma shawarci daliban da ke zaune a wajen makarantar da su kasance a gida a wannan lokacin."

Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe

Kungiyar fafutukar kare hakkin musulmai (MURIC) ta yi kira da a gaggauta kame gaba ɗaya waɗanda suka aikata kisan musulmai matafiya a Jos, inda ta kira su da "Mayakan kiristoci a Jos."

Kara karanta wannan

Yar JSS 1 ta shigar da gwamnatin Ekiti kotu don an zaneta, ta bukaci a biyata N15m

Daily Nigerian ta ruwaito cewa matafiya musulmai 25 wasu sojojin ƙungiyar kiristanci suka kashe a Rukaba, jihar Filato ranar Asabar.

A wani jawabi da daraktan MURIC, Ishaq Akintola, ya fitar, ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa musulmai, tare da kira ga gwamnati ta kame waɗanda suka aikata kisan.

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

A wani labarin, Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.

Wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.

Kara karanta wannan

Twitter ta yi martani bayan gwamnati ta sanar da dage dokar haramtata a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel