Yar JSS 1 ta shigar da gwamnatin Ekiti kotu don an zaneta, ta bukaci a biyata N15m

Yar JSS 1 ta shigar da gwamnatin Ekiti kotu don an zaneta, ta bukaci a biyata N15m

  • Yar ajin fakro a makarantan sakandare ta shigar da gwamnatin Ekiti kotu don an zaneta
  • Dalibar ta bukaci gwamnatin jihar ta biyata diyyar N15m don cin mutuncin da akayi mata
  • Wannan ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta

Wata dalibar JSS 1, Gift Agenoisa, ta shigar da makarantar da take zuwa Mary Immaculate Secondary School, dake Ado- Ekiti, gaba kuliya, kan bulalan da akayi mata.

Hakazalika, dalibar ta bukaci babbar kotun jihar ta wajabtawa makarantar biyanta N15m na raunin da aka ji mata sakamakon bulalan da kuma dakatar da ita da akayi.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa a kara mai lamba HAD/01/CR/2021, dalibar ta ce dakatar da ita da aka yi danne hakkinta ne.

Tace na ci mata mutunci a makarantar kawai don ta je makarantar da wani irin kitso na daban.

Kara karanta wannan

Dalibar aji 1 a sakandire ta maka gwamnatin Ekiti a kotu, tana bukatar diyyar N15m

Daga cikin wadanda ta shigar kara akwai shugabar makarantar, Mrs Oluwasanmi F.M; kwamishanan ilimi, Dr Olabimpe Aderiye; hukumar makarantun jihar Ekiti, da gwamnatin jihar Ekiti.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yar JSS 1 ta shigar da gwamnatin Ekiti kotu don an zaneta, ta bukaci a biyata N15m
Yar JSS 1 ta shigar da gwamnatin Ekiti kotu don an zaneta, ta bukaci a biyata N15m Hoto: Channels Tv
Asali: Twitter

A takardar rantsuwar da tayi a kotu, dalibar tace a ranar 22 ga Mayu, an fitar da ita cikinsauran dalibai kuma shugabar makarantar ta bada umurnin yi mata bulala 20 kan kitso mara kyau.

Ta bukaci a mayar da ita makaranta ba tare da wani tsangwama ba.

Sai da aka kwantar da ita a asibiti sakamakon bulalan

Tace sakamakon bulalan da akayi mata, ta samu raunuka iri-iri da jini a jikin kayan makarantarta kuma sai da ta suma aka garzaya da ita asibitin yan sanda a Ado-Ekiti.

Ta kara da cewa tun lokacin, an hanata shiga makaranta.

A ranar 22 ga Mayu, mahaifin dalibar wanda jami'in dan sanda ne, Elijah, ya tura gardawan yan sanda hudu suka ci mutuncin wasu Malamai don sun zane diyarsa saboda an ladabtar da ita.

Kara karanta wannan

Ban nemi kotu ta kori Buni a matsayin Gwamnan Yobe ba - Dan takarar gwamnan PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel