MURIC: Gwamna Zulum ya sake gina wasu coci-coci guda 9 da Boko Haram ta lalata

MURIC: Gwamna Zulum ya sake gina wasu coci-coci guda 9 da Boko Haram ta lalata

  • A karo na biyu, MURIC ta sake bincike kan yadda gwamna Zulum ya yi wa Kiristocin Borno adalci
  • MURIC ta gano cewa, gwamnan ya sake gina coci-coci guda tara da Boko Haram suka lalata a baya
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka zargi gwamna Zulum da rushe coci-coci da dama a fadin jihar

Borno - Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta Muslim Rights Concern (MURIC), ta sake caccakar masu suka da zargin gwamnatin jihar Borno da rashin yi wa Kiristoci adalci, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan rushe cocin EYN da aka yi a makon da ya gabata a Maiduguri, babban birnin jihar, da yawa sun soki gwamnatin jihar bisa wannan aiki.

Sai dai, MURIC, a ranar Talata, ta ce bincike ya nuna cewa gwamnatin jihar ta rusa masallatai fiye da coci-coci, sabanin ikirarin cewa wuraren ibada na kirista ne kawai aka rusa.

MURIC: Gwamna Zulum ya sake gina wasu coci9 da Boko Haram ta lalata
Daraktan MURIC Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Kungiyar ta ce karin bincike ya nuna cewa coci-coci tara da mayakan Boko Haram suka lalata tun a watan Disambar 2020, gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sake gina su.

Kara karanta wannan

Mun fidda mutum milyan 10 daga cikin talauci a shekaru shida, Gwamnatin tarayya

A wani sabon rahoton, Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce:

“Baya ga binciken farko na cewa an rushe masallatai fiye da coci-coci, masu bincikenmu sun gano wani abin mamaki, wato gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sake gina coci -coci tara, dukkansu mallakar EYN ne, wanda Boko Haram suka kai hari suka lalata su a watan Disamba na 2020.

Jerin coci-coci da gwamna Zulum ya sake ginawa

A sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Daily Nigerian, Daraktan MURIC ya lissafo dukkanin coc-coci tara da gwamnan ya sake gina wa wadanda suke a Hawul, Chibok da Askira-Uba a Borno.

Sune kamar haka:

  1. EYN LCC Ghung
  2. EYN LCC Sangyere
  3. EYN LCC Kirbutu
  4. EYN LCC Tashan Alade
  5. EYN LCC Shidifu
  6. EYN LCC Azare
  7. EYN LCC Kwajaffa
  8. EYN DCC Yawa Wamdeo
  9. EYN LCC Piyami

MURIC ta kuma gano cewa, gwamnan ya ziyarci yankunan da abin ya faru tun lokacin da aka ba da labarin faruwarsu.

Kara karanta wannan

Masallatan da Gwamna Zulum ya rusa sun fi cocina yawa – Kungiyar MURIC

Rushe coci a Maiduguri: An sheke mutum 1 yayin arangama, Zulum ya magantu

A wani labarin, Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi Allah wadai da wani rikici wanda yayi sanadiyyar rushe wata coci kuma ya umarci ‘yan sanda su yi bincike akan lamarin.

A kalla mutum daya ne ya rasa ransa yayin da mutane da dama suka samu miyagun raunuka bayan taron ‘yan kungiyar BOGIS sun budewa fararen hula huta yayin da suke rushe wata cocin EYN dake wuraren Maduganari dake babban birnin Maiduguri.

PRNigeria sun tattara bayanai akan yadda wasu fusatattun matasa wandanda sakataren BOGIS, Adam Bukar-Bababe ya jagorancesu sannan suka fara rushe cocin ba tare da an yi aune ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel