Abinda Shugaba Buhari Zai Fara Yi Bayan Dawowarsa Daga Landan, Femi Adesina

Abinda Shugaba Buhari Zai Fara Yi Bayan Dawowarsa Daga Landan, Femi Adesina

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaba Buhari zai fara neman sanin inda aka kwana bayan dawowa daga Landan
  • Kakakin shugaban, Femi Adesina, yace mataimakin shugaba da kuma manyan jami'ai zasu gabatar da komai ga Buhari
  • A cewarsa abubuwa da dama sun faru yayin da ya tafi landan na tsawon mako uku a ɓangaren tsaro da sauransu

Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, zai fara karbar bayanai daga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, da makusantansa bayan dawowarsa Najeriya.

Shugaba Buhari, ya diro Najeriya ranar Jumu'a da yamma a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe, Abuja, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Buhari ya kwashe kusan makwanne uku a tafiyar da ya yi zuwa Birnin Landan domin halartar taron haɓɓaka Ilimi na duniya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida bayan kimanin makonni biyu a Landan

Lokacin da manyan jami'an gwamnati suka tari Shugaba Buhari
Abinda Shugaba Buhari Zai Fara Yi Bayan Dawowarsa Daga Landan, Femi Adesina Hoto: Buhari Sallai FB Fage
Asali: Instagram

Wane abu Buhari zai fara maida hankali?

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana abinda Buhari zai fara maida hankali a kai da zaran ya shiga ofis a wata fira da Channels TV cikin shirin Politics Today.

Adesina yace:

"Da farko zai fara karbar bayanai daga mataimakin shugaban ƙasa da kuma manyan jami'an gwamnatinsa. Zasu masa bayani dalla-dalla kan abinda ya faru cikin mako uku da baya nan."
"Kuma kun sani a ɓangaren tsaro abubuwa da dama sun faru. Yadda ake kara samun nasara kan yan ta'adda, yan bindiga, akwai abubuwa da yawa da zasu yiwa shugaban bayani."
"Bayan haka akwai ayyukan cigaba da gwamnati ke yi, ku na ganin yadda ministan ayyuka yake zuwa duba aikin ya na kaddamar da wasu."

A wani labarin kuma gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ya bayyana yadda yake shan matsin lamba daga iyalai da abokan arziki kan takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin wasu ƙungiyoyi dake neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023.

Muhammed, wanda ya nemi a bashi mako 3 ya yi shawara, ya sake neman a sake ba shi lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel